Bala Muhammad ya zama shugaban gwamnonin jam’iyyar PDP

An zaÉ“i gwamnan jihar Bauchi, Bala Muhammad a matsayin sabon shugaban kungiyar gwamnonin jam’iyyar PDP.

Siminalayi Fabura zaɓaɓɓen gwamnan jihar Rivers shi ne mataimakin shugaban kungiyar.

Muhammed da Fubara an zaÉ“e su ne a ranar Asabar a wurin wani taron sanin makamar aiki da aka yi wa waÉ—anda aka zaÉ“a a Æ™arÆ™ashin jam’iyar PDP da aka gudanar a Bauchi.

Da yake magana a wurin taron shugaban riko na jam’iyyar PDP, Umar Damagum ya shawarci mambobin da su haÉ—a kai suyi aiki tare a matsayin Æ´an uwa.

Muhammed zai maye gurbin gwamnan jihar Oyo, Seyi Makinde wanda ya zama mataimakin shugaban kungiyar gwamnonin Najeriya.

More News

An sako wani alƙali a jihar Borno bayan shafe wata biyu a hannun ƴan bindiga

An sako mai Shari'a Haruna Mshelia alƙalin babban kotun jihar Borno wanda aka ɗauke a cikin watan Yuni. Daso Nahum mai magana da yawun...

Atiku ya yi Allah-wadai da ƙarin haraji a Najeriya

Tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar ya yi Allah-wadai da shirin da gwamnatin tarayya ke yi na kara haraji.  A wata sanarwa da Atiku...

Ina jin ƙwarin gwiwar cin zaɓe a 2027—Kwankwaso

Jagoran jam'iyyar New Nigeria Peoples Party (NNPP) na kasa, Rabi'u Kwankwaso, ya bayyana fatansa game da makomar jam'iyyar a zaben shugaban kasa na 2027...

HaÉ—arin tankar mai ya yi ajalin mutane kusan 30 a Neja

Fashewar wata tankar mai ta yi sanadiyyar mutuwar mutane 30 a hanyar Agaie-Bida a jihar Neja da safiyar LahadiRahotanni sun tattaro cewa tankar ta...