Ba Za A Samu Matsalar Karancin Man Fetur Ba – NNPC

Dogayen layuka a gidajen mai na daga cikin alamun da ‘yan Najeriya ke la’akkari da su wajen yiwuwar samun karancin man fetur a kasar.

Kamfanin man fetur na Najeriya NNPC ya ba da tabbacin cewa kasar na da wadataccen mai a ajiye wanda zai iya biyan bukatun daukacin ‘yan Najeriya.

NNPC ya fitar da wannan sanarwa ce a ranar Laraba bayan da layukan mai suka fara kunno kai a Abuja, babban birnin kasar.

Sai dai cikin sanarwar mai dauke da sa hannun Babban Manajan yada labaran kamfanin Garbadeen Muhammad, NNPC ya yi kira ga jama’a da su kwantar da hankulansu.

“Kamfanin NNPC na mai sanar da ku cewa yana da wadataccen mai a ajiye wanda zai biya bukatun ‘yan Najeriya.

“Muna kira ga jama’a da kada su yi ta tururuwar sayen man, su yi watsi da jita-jitar da ke nuna cewa za a samu karancin man.” Garbadeen Muhammad ya ce.

‘Yan Najeriya dai kan yi rige-rigen sayen man fetur su ajiye, a wani mataki na kandagarki, idan sun ga alamu da ke nuna cewa za a samu karancin man.

Dogayen layuka a gidajen mai na daga cikin alamun da ‘yan Najeriya ke la’akkari da su wajen yiwuwar samun karancin man fetur a kasar.

More News

Kwankwaso ya ziyarci Obasanjo

Tsohon gwamnan Kano, Rabiu Musa Kwankwaso ya ziyarci tsohon shugaban kasa, Olusegun Obasanjo. Ziyarar ta Kwankwaso wani bangare ne na cigaba da tattaunawar...

Kwankwaso ya ziyarci Obasanjo

Tsohon gwamnan Kano, Rabiu Musa Kwankwaso ya ziyarci tsohon shugaban kasa, Olusegun Obasanjo. Ziyarar ta Kwankwaso wani bangare ne na cigaba da tattaunawar...

Sojojin sun kama tarin makamai a a hannun mayakan IPOB

Rundunar sojan Najeriya ta samu nasarar kama makamai da suka hada bindigogi hodar hada bam a jihar. Rundunar ta samu gagarumin wannan nasara ne biyo...

Atiku ya ziyarci mahaifiyar su Yar’adua

Mai neman takarar shugaban kasa a jam'iyar PDP, tsoshon mataimakin shugaban kasa, Alhaji Atiku Abubakar ya ziyarci mahaifiyar tsohon shugaban kasa, Umar Musa Yar'adua...