Ba tasirin da ayyukan mazabu suka yi a shekaru 10, inji Buhari

Shugaba Buhari

Hakkin mallakar hoto
Buhari Sallau

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya bayyana damuwa kan rashin ganin sakamakon a-zo-a-gani daga dumbin kudaden da ‘yan majalisun tarayya suka kashe don ayyukan mazabu fiye da naira tirliyan daya, a tsawon shekara goma.

Shugaba Buhari da ke jawabi a wani taron yaki da cin hanci da rashawa a ma’aikatun gwamnati ya ce bayanan da ya karba kan ayyukan mazabu a yankunan karkara sun nuna cewa ayyukan ba wani tasiri da suka yi ga al’umma.

Shugaban ya ce rahoton ICPC da aka gabatar ma shi ya tabbatar da yadda mutanen karkara ba su ci moriyar makudan kudaden da aka ware ba domin ayyukan mazabu na ‘yan majalisu.

An dade dai ana zargin ‘yan majalisar na fakewa da sunan ayyukan raya mazabu wajen cusa wasu kudade a cikin kasafin kudi, inda suke zagawa su yi kashe-mu-raba da ‘yan kwangila.

Sai dai ‘yan majalisar sun dade musanta wannan zargi, saboda a cewarsu ba su da kusanci da yadda ake aiwatar da ayyukan raya mazabun.

Sanata Kabiru Marafa daga Zamfara ta tsakiya wanda kafin zaben 2019, ya shafe tsawon shekara takwas a majalisar dattijai, duk da bai musanta ikirarin shugaban na Najeriya ba amma ya ce kamar yadda ake zargin ‘yan majalisa dole a zargi bangaren zartarwa.

Ba dan majalisa ke daukar kudi ya gudanar da aiki ba, a ma’aikata yake kai kudin wanda shugabanta karkashin shugaban kasa yake.

Sanatan ya ce babu wani tsari a Najeriya kan irin ayyukan da ya kamata dan majalisa ya gudanar. “Idan shugaban kasa yana son sauyi sai ya fito da sabon tsari ta yadda za a yi ayyukan da za su amfani jama’a.”

Shugaban Buhari dai ya dade yana nanata cewa cin hanci da rashawa ne babban matsalar Najeriya wanda ke haifar da talauci da matsalar tsaro da tabarbarewar ilimi da kiwon lafiya da sauran abubuwan ci gaban ga al’umma.

Ya ce gwamnatinsa za ta ci gaba da bincike kan duk wani dan kwangila da ma’aikacin gwamnati da aka samu da karkatar da kudaden da aka ware domin ayyukan mazabu.

Kuma ya ce gwamnatinsa na iya kokarinta wajen shawo kan matsalar musamman a ma’aikatun gwamnati.

Shugaba Buhari ya ce yanzu gwamnati za ta sa ido kan ayyukan mazabun na ‘yan Majalisa inda za a sanar wa ‘yan kasa yawan kudaden da aka ba dan majalisa.

More News

Sojoji Sun Ceto Lydia Simon Ɗaya Daga Cikin Ƴan Matan Chibok

Dakarun sojan Najeriya dake aiki da rundunar samar da tsaro ta Operation Desert Sanity III sun samu nasarar ceto, Lydia Simon É—aya daga cikin...

Gwamna da ƴansanda sun daƙile yunkurin EFCC na kama Yahaya Bello

A ranar Laraba ne Gwamnan Jihar Kogi, Usman Ododo, ya dakile wani yunkurin da Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arzikin Kasa Ta’annati ta...

Gwamnatin Tarayya Za Ta Fara Rabon Gidaje 8925

Gwamnatin tarayya ta ce ta fara raba gidaje 8925  ga mutanen da suka nema kuma suka cancanci a basu a faɗin ƙasa baki ɗaya...

Ƴan Bindiga A Zamfara Sun Kashe Sakataren Jam’iyar PDP

Wasu ƴan bindiga da ba a san ko suwaye ba sun kashe, Musa Ille  sakataren jam'iyar PDP na ƙaramar hukumar Tsafe a jihar Zamfara. Zagazola...