Ba sauran sulhu tsakaninmu da ‘yan bindiga sai kisa – Matawalle

Matawalle

Asalin hoton, Zamfara Gov

Gwamnan Jihar Zamfara da ke arewacin Najeriya Bello Matawalle ya ce ‘yan bindiga sun yi watsi da damar da suka samu ta sulhu a baya, yanzu tsakanin gwamnati da su sai aikawa lahira.

Cikin wani bidiyo da ke ta yawo a kafafen sada zumunta, an ga Gwamna Matawalle yana jawabi a wani masallaci bayan idar da sallah, inda yake yi wa al’umma bayani kan halin da ake ciki a jihar.

Matawalle ya ce “gaskiyar magana suna shan wuta sosai, ko jiya an turo kwamiti babba a sameni, cewa in tsagaita don Allah, in saki a rika samun abinci na ce wallahi ba zan saki ba,”.

“Duk wani abu da Allah ya ce muyi munyi, saboda haka mun yi iyakar yinmu, yanzu abin da muke yi shi ne mu sada su da ubangijinsu su amsa tambayoyi ga Allah.”

A watan Fabirairu, Gwamnan ya ce sulhu da ‘yan bindigar ne zabi na karshe da ya rage domin shawo kan matsalar tsaro a Najeriya.

Amma a yanzu Gwamnan ya ce matakin yakarsu ba dare ba rana suka dauka domin sun ki amfani da damar da aka ba su.

Ya rarrashi mutanen jihar da su yi hakuri game da datse layukan waya da aka yi a fadin jihar, an yi ne domin samar da zaman lafiya mai dorewa ga al’ummar jihar Zamfara.

Matawalle ya ce in Allah ya yarda Zamfara za ta samu lafiya, don haka a shirye yake ya sha walaha tare da mutanen jihar domin a gudu tare a tsira tare.

“Idan aka daina shigar da abinci da itace da man fetur da kuma amfani da babura ‘yan bindigar za su fito su rika mika kansu da kansu.

“Yan siyasa su ji tsoron Allah su daina sayan babura suna raba wa mutane, wadanda su kuma daga baya suke sayar wa wadannan miyagu.” in ji Matawalle.

Gwamnan ya ce yanzu ‘yan bindigar na tserewa zuwa wasu jihohi da ke makwabtaka domin wuyar da suke sha a jihar Zamfara.

Wuya ce ta dan lokaci da idan aka jure mata za ta samar da kwanciyar hankali a cewarsa.

Jihar Zamfara na daya daga cikin jihohin da ke fama da ayyukan ‘yan bindiga da masu garkuwa da mutane a Najeriya.

Wannan ne ya sanya gwamnatin Jihar ta dauki wasu matakan dakile wannan matsala, ta hanyar hana fitar da dabbobi daga jihar baki daya.

(BBCHausa)

More News

EFCC na neman Yahaya Bello ruwa a jallo

Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arzikin Kasa Ta’annati (Economic and Financial Crimes Commission) ta bayyana tsohon gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello a matsayin...

Mutane da dama sun mutu bayan motar fasinja ta taka bam a Borno

Akalla mutane 16 ne ake fargabar sun mutu yayin da wasu 20 suka jikkata bayan wata motar fasinja da ke kan titin Baga-Kukawa a...

Sojoji Sun Ceto Lydia Simon ĆŠaya Daga Cikin Ćłan Matan Chibok

Dakarun sojan Najeriya dake aiki da rundunar samar da tsaro ta Operation Desert Sanity III sun samu nasarar ceto, Lydia Simon É—aya daga cikin...

Gwamna da ƴansanda sun daƙile yunkurin EFCC na kama Yahaya Bello

A ranar Laraba ne Gwamnan Jihar Kogi, Usman Ododo, ya dakile wani yunkurin da Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arzikin Kasa Ta’annati ta...