Ba halina ba ne ku yafe min – Sanata Abbo | BBC Hausa

Senator Elisha Abbo win election on February 23, 2019 as Senator representing senatorial senatorial district
Hakkin mallakar hoto
Elisha Abbo
Image caption

Sanata Elisha Abbo na jam’iyyar PDP yana wakiltar shiyyar arewacin jihar Adamawa ne

Dan majalisar dattijan wanda bayanai suka ambato shi cike da nadama a taron manema labaran da ya yi cikin shalkwatar jam’iyyarsa ta PDP da ke Abuja, ya nemi gafara, kuma ya ce a yafe masa.

Sanata Elisha Abbo, wanda ke wakiltar shiyyar arewacin jihar Adamawa, ya ce “ba halina ba ne tozarta mata, don haka na yi nadama”.

Faifan bidiyon dai ya tayar da kura da kuma janyo tofin Allah-tsine daga masu fafutuka da dumbin ‘yan Najeriya har ma da fitattun ‘yan siyasa musamman a shafukan sada zumunta.

Rundunar ‘yan sandan Najeriya ta ce ta fara gudanar da bincike kan zargin cin zarafin matar.

Lamarin ya faru ne a wani shagon sayar da kayan wasannin jima’i da sanatan ya ziyarta tare da rakiyar wasu mata.

A taron manema labaran da ya yi, Sanata Abbo ya ce “Ba na zo nan ba ne don yin bayani kan abin da ya faru ta bangarena. Na zo ne don neman afuwar ‘yan Najeriya saboda bata musu rayukan da na yi.”

“Cikin matukar nadama da sanin ciwon kai, ni Ishaku Abbo nake matukar neman gafarar duk ‘yan Najeriya da majalisar dattijai da jam’iyyar PDP da iyalina da abokaina da kuma uwayenmu, matan Najeriya.

Ni da kaina kuma ina neman afuwar Bibra[wacce ya ci zarafi], da danginta saboda abin da na yi. Duk ma dai abin da kika yi mini, ba ki cancanci irin wannan mataki ba, ki yi hakuri!” In ji Matashin sanatan mai shekara 41.

Ya kamata PDP ta dauki mataki a kansa

Bidiyon dan majalisar a shagon sayar da kayan wasannin jima’i da ke ikirarin nuna shi yana dukan mai tsaron kanti, ya janyo fushi da bacin rayuka.

Mutane da dama ciki har da dan takarar shugaban kasa na baya-bayan nan a jam’iyyar PDP Atiku Abubakar suka bukaci a gurfanar da shi gaban hukunci tare da neman majalisar dattijai ta koya masa ladabi.

A wani sako da ya wallafa a shafinsa na Twitter, Atiku ya ce kamata jam’iyyar PDP ta dauki matakin ladaftarwa a kan sanatan.

“Ina shawartarsa da ya fito fili ya nemi afuwa sannan ya mika kansa ga ‘yan sanda domin ya nuna dattako.

“Sannan kuma ina kira ga uwar jam’iyyarmu ta PDP da ta dauki matakin ladaftarwa a kansa, su ma ‘yan sanda su tabbatar cewa doka ta yi aikinta.”

Afuwar da sanatan ya nema ta zo ne sa’o’i kadan bayan kiran da Atiku Abubakar ya yi masa na ya yi hakan.

Rundunar ‘yan sandan kasar ta alkawarta sanar da ‘yan Najeriya sakamakon bincike da ta fara gudanarwa.

Ita ma majalisar dattijan kasar ta kafa kwamiti domin ya binciki wannan batu a daidai lokacin da jam’iyyarsa ta PDP ta fito ta yi Alla-wadai da halayyar cin zarafin da ake zargin sanatan ya yi wa wannan mata mai shayarwa.

More News

Majalisar dokokin jihar Kaduna ta nemi ma’aikatar kudin jihar ta miÆ™ata bayanan bashin da El-Rufai ya ciwo

Majalisar dokokin jihar Kaduna ta nemi ma'aikatar kudi ta jihar da ta miƙa mata cikakken bayani kan basukan  da gwamnatin tsohon gwamnan jihar, Nasiru...

An dakatar da ayyukan kamfanin jiragen sama na Dana Air

Festus Keyamo, ministan harkokin sufurin jiragen sama ya umarci hukumar FAAN dake lura da sufurin jiragen sama a Najeriya ta dakatar da ayyukan kamfanin...

Yahaya Bello Ya Bayyana Dalilan Da Ya Hana Shi Bayyana A Gaban Kotu

Tsohon gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello ya ce tsoron kamun  hukumar EFCC dake yaÆ™i da yiwa tattalin arzikin Æ™asa ne ya hana shi bayyana...

Ƴan sanda sun kama mutane biyu dake samarwa ƴan fashin daji makamai a jihar Kaduna

Rundunar Æ´an sandan jihar Kaduna ta ce tana tsare da wasu mutane biyu da ake zargi da safarar bindiga a jihar. A wata sanarwa ranar...