Ba a hana karbar karbar tsoffin kudi a Najeriya ba – CBN

Babban Bankin Najeriya

Hakkin mallakar hoto
TWITTER

Image caption

Babban Bankin Najeriya bai sa wa mutane wa’adin kin karbar kudi ba a tsakaninsu, illa ya hana bankuna ba wa jama’a tsoffin kudin ne kawai

Yayin da wasu ‘yan Najeriya suka shiga rudani dangane da wata jita-jitar cewa za a daina karbar tsofaffin takardun kudi a bankunan kasar nan da dan wani lokaci, wani babban jami’i a daya daga cikin manyan bankunan kasar ya ce mutane sun yi kuskuren fahimtar lamarin.

Bincike ya nuna cewa jita-jitar ta sa wasu har karyar da darajar kudadensu suke yi, wadanda suke ganin sun tsufa, inda wasu kan bayar da misali naira dubu daya a ba su kamar naira dari bakwai, ko wani abu na kamar naira dari bakwai ko ma kasa da haka.

A wata hira da BBC ta yi da wani babban darakta a daya daga cikin bankunan kasuwancin na kasar, ya ce a umarnin da babban bankin kasar ya ba su babu inda aka ce su sanya wani wa’adi na daina karbar tsohon kudi.

Mallam Haruna Musa, na bankin Guarantee Trust Bank, wato GT, ya ce mutane ba su fahimci batun ba yadda ya kamata, shi ya sa ake ta yada wannan jita-jita.

Jami’in ya ce babban bankin kasar ne ya zo da tsari domin kyautata yanayin takardun kudin da jama’a ke amfani da su kasancewar karuwar jama’ar da kasar ke da su, da suka kai kusan miliyan dari biyu.

A don haka ne ya ce babban bakin ya bayar da umarni ga dukkanin bankunan kasar da idan za su ba wa mutane ko masu mu’amulla da su kudi, kada su sake ba su tsohon kudi.

Kuma a duk lokacin da wani mutum ya kai wa bakin takardun kudi komai lalacewarsu, idan dai har za a iya ganin lambar kudin ko ta gaba ko ta gaya, to banki ya tabbatar ya karba kuma ya musanya wa mutum da sabo.

Daraktan ya ce wa’adin da ake magana a kai, babban bankin Najeriyar ne ya dora wa bankunan kasuwanci cewa ya dage cajin da yake musu na naira dubu 12 a duk akwati daya da suke kaiwa mai dauke da kudi misali tsoffin kudi, a tsawon wata uku.

Amma bayan wannan wa’adi na wata uku babban bankin zai ci gaba da karbar ladan na naira dubu 12 da yake karba da aikin da zai yi musu idan sun kai akwatin da ke dauke da tsoffin kudi, amma ba wai za a daina karbar kudin ba ne.

Jami’in ya ce domin a karfafa wa bankuna guiwa ne domin su rika kai tsoffin takardun kudin ne, babban bankin kasar ya cire musu wannan haraji da suke biya, na tsawon wata uku, wa’adin da zai kare ranar uku ga watan Satumba din nan.

Darektan ya kara da cewa, a ka’ida duk mutumin da yake da wata takardar kudi ko ta nawa ce, walau naira biyar ce kawai ko goma ko ashirin ko abin da ya fi haka, zai iya shiga kowane banki, ba sai yana da wani asusun ajiya a bankin ba, ya nemi a canja ma sa, ba tare da an rage ma sa ko kobo ba, kuma duk bankin da ya ki karba ma, babban bankin kasar zai hukunta shi ne a bisa doka.

Baya ga haka ma, ya ce ko da ta nau’rar karbar kudi ta ATM, banki ya ba wa mutum tsohon kudi yana da damar ya shiga cikin bankin a sauya ma sa, idan har bankin ya ki to hukunci zai hau kan bankin.

More News

EFCC na neman Yahaya Bello ruwa a jallo

Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arzikin Kasa Ta’annati (Economic and Financial Crimes Commission) ta bayyana tsohon gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello a matsayin...

Mutane da dama sun mutu bayan motar fasinja ta taka bam a Borno

Akalla mutane 16 ne ake fargabar sun mutu yayin da wasu 20 suka jikkata bayan wata motar fasinja da ke kan titin Baga-Kukawa a...

Sojoji Sun Ceto Lydia Simon ĆŠaya Daga Cikin Ćłan Matan Chibok

Dakarun sojan Najeriya dake aiki da rundunar samar da tsaro ta Operation Desert Sanity III sun samu nasarar ceto, Lydia Simon É—aya daga cikin...

Gwamna da ƴansanda sun daƙile yunkurin EFCC na kama Yahaya Bello

A ranar Laraba ne Gwamnan Jihar Kogi, Usman Ododo, ya dakile wani yunkurin da Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arzikin Kasa Ta’annati ta...