Aure: Yadda zamani ya sauya al’adar kukan amare zuwa gidan miji

Wasu ma ganin amaren yanzu ba sa kuka saboda sna iya magan da iyayensu a kodayaushe suke so ta hanyar waya

Hausawa kamar sauran al’umomi na duniya, mutane da ke da al’adu daban-daban da suka shafi gudanar da rayuwarsu.

Wasu daga cikin al’adu sun shafi yadda ake bikin aure; a ciki har da al’adar da ta shafi yadda amarya take rusa kuka, ta rika guje-guje da zarar za a kai ta gidan nijinta.

A wasu lokutan ma ko bayan an kai ta gidan mijin ba ta sauya zane, domin za ta rika guduwa ana kamo ta ana dawo da ita, ko kuma ta rika kin walwala da cin abinci, sai dai kuka.

Duk da yake wannan dadaddiyar al’ada ce sai dai yanzu ana ganin an soma juya mata baya.

Hausawa wadanda shekarun suka ja sun san yadda wannan a’l’ada ta yi tasiri a zamantakewar aure da ta iyali.

Ko mene ne yake sanya amarya kuka? Shin al’adar tana gushewa ne? Idan hakan ne, me ya sa?

Wadannan su ne wasu daga cikin batutuwan da wannan makala ta fito da su.

Alhaji Mahammadu Umar Mai-Zabura, wani dattijo ne a Maiduguri wanda ya bayyana wa BBC cewa aure wani muhimmin abu ne a cikin rayuwar kowace al’umma, domin shi ne tubalin gina zuriya a kan kyakkyawar hanya da kuma tushe.

Ya ce don haka yana da matukar muhimmanci ga ko wace al’umma ta duniya, ya zamanto alakar rayuwarsu ta zamantakewa tsakanin mace da namiji ta kasance ana gina ta a hanyar auratayya don samun karbuwa a al’adance da kuma addini.

”Ko wace al’umma tana gudanar da harkokin auratayya bisa manufa da kuma tsarin da ta ga ya dace da ita,” in ji Mai-Zabura.

A cewarsa, akwai dumbin dalilai da suka sanya wa amarya take kuka “kuma sun danganta ne ga yanayin yadda aka bi aka aurar da yarinya, da galibi hakan a auren fari ne yakan faru.”

Wadanne dalilai ne ke sa amare kuka?

Dalilan dai kamar yadda galibin mutane ke fada suna da nasaba da kewar gida da ‘yan matan ke tunanin yi da zarar sun bar iyayensu.

”Suna jin kunya da fargabar haduwa da wadanda ba iyayensu ba, da dangin da ba nasu ba, suna jin kunyar an hada su da wani namiji , kana suna ganin an raba su da iyayensu, da yan uwansu da kawayensu, zama dandali da suka saba, duk hakan na sa amare yin kuka,” in ji Mai-Zabura.

Ya kara da cewa: ”A wasu lokuta ma nisa da gida ko garin da yarinya take shi yake kara sa amarya ta rika kuka, don za ta hadu da wata sabuwar rayuwa da ba ta saba da ita ba kuma a inda take fargabar za ta dade bata ga iyayenta da danginta ba.”

Hajiya Amina Saulawa da ke jihar Katsina ta shaida wa BBC cewa a baya yakan kasance a wasu lokutan ita yarinyar ba ta ma san wanda za a aura mata ba, don haka babu shakuwa a tare a tsakaninsu, shi ya sa yarinya kan rika kuka idan za a kai ta gidan miji.

“Amaren kan rika kuka ne saboda galibi wasu a lokacin ba su riga sun mallaki hankalinsu ba, saboda karancin shekaru, ba su fahimci mecec e rayuwar aure ba, sannan ga rabuwa da iyaye,” in ji Amina.

Kwana a kabarurruka da kan bishiya

Ita kuwa malama Rahinatu Abubakar cewa ta yi gaskiya zamanin da da na yanzu akwai bambanci sosai wajen al’adar kukan da amare ke yi lokacin da za a kai su gidan miji.

Rahinatu ta ce ” Dalilan da suka sa amarya ke kuka lokacin da za a kaita gidan miji sun hada da tsoron inda za a kai ta, don bata san me zata tarar ba, ga kuma alhinin rabuwa da iyaye”.

”Shekaruna 12 lokacin da aka yi min aure aka kai ni can garin Bidda jihar Niger, kuma bayan an kai ni na rika guduwa makabarta ina kwana, na ka tada kai da kabari in yi barci na,” ta ce.

”Daga bisani da na ga alamu ana fako na sai na koma hawa kan bishiyar mangwaro ina kwana, don kawai ina gudun gidan miji,” in ji ta.

Amma kuma ta ce yanzu lamarin ya sauya, sai dai kuma duk da haka akwai daidaikun wurare da har yanzu ake samun irin wannan al’ada ta kukan aure.

Hakan na faruwa ne in ji ta saboda a yanzu ana barin yara mata su yi karatu mai zurfi wanda hakan yakan sa su kara mallakar hankalinsu kafin a yi musu aure.

Ta kuma kara da cewa ”Babban dalilin kukan shi ne saboda ka saba da gidanku, da mahaifanka, da ‘yan uwanka, kuma ka san cewa idan ka tafi shikenan sai lokaci mai tsawo, kuma a wasu lokutan akan kai yarinya wani gari ne mai nisa.”

Ita ma a nata ra’ayin wata dattijuwa Hajiya Fatima Haruna cewa ta yi batun haka yake, yawanci kukan rabuwa da iyaye da dangi ne sassala, duk da cewa akwai sauran dalilai da kan sa kukan.

”Shekaruna 13 lokacin da aka yi mini aure, kuma iyayena ne suka zabar min suka ce sai Bafulatani dan uwana,” in ji ta.

Ta kuma bayyana cewa a lokacin da aka kai ta gidan miji surukarta ce ta rika kula da ita, sai bayan wata daya sannan ta ga mijin da aka aura mata.

Sai dai kuma wasu dalilan da suka sa yanzu ba a cika samu irin wannan al’ada da kukan tafiya gidan miji ba shi ne saboda abubuwan sauye-sauye da zamani ya kawo wadanda suka hada da ci gaba a fannin sufuri, baya ga bunkasar hanyoyin sadarwa irin su wayar salula da kuma hanyoyi daban-daban da a ko ina kake a duniya kamar kana tare da mutum.

Malama Surayya Aminu wata matashiya ce da a shekarun baya aka yi mata aure, kuma ta shaida wa BBC cewa ita ba ta taba sanin ma akwai wata al’adar da ake kuka idan za a tafi gidan miji ba.

”Ni kam na sai bayan da na kusa kammala karatun jami’a aka yi min aure, na san babu dadi rabuwa da iyaye da ‘yan uwa, amma kuma na san komai dadewa zan bar su, don haka mene ne abin kuka tun da auren soyayya muka yi?,” in ji ta.

Ta kuma ce: ”Ai ko a ina ne tun da akwai kafofin sadarwa a koda yaushe ina iya magana da iyayena da ‘yan uwana, ko da kuwa hira da bidiyo ne muna ganin juna kamar muna tare, don haka babu wata damuwa”.

Halima Sani kuwa ta cewa ta yi lokacin da aka yi mata aure na soyayya tana da shekara 21, amma duk da hakan sai da ta yi kukan rabuwa da iyayenta.

”Ina son mijin da aka aura min, auren soyayya ne, ina ta murna amma kuma ranar da za a kai ni gidansa sai da hankalina ya tashi, sai wani tunani ya zo min na ga cewa zan fara wata rayuwa da ban sani ba, kuma zan daina ganin iyayena, da ‘yanuwana kamar yadda na saba,” a cewarta.

Auren dole ko na zabin iyaye?

Irin wannan aure ne wanda akan nema wa yaro ko yarinya daga cikin dangin uwa ko na uba ba tare da neman shawararsu. Irin wannan aure ana yin sa ne don kara dankon zumunci tsakanin ‘yanuwa.

Ta wani gefen kuma iyayen yarinya kan aurar da ita ga wani saboda matsayinsa, ko kudinsa, ko da kuwa ba ta son shi.

Duka irin wadannan suna saka amare kuka da guje-guje idan za a kai su gidan miji, kamar yadda Hajiya Amina Saulawa ta shaida wa BBC.

Duk da cewa al’amura sun kara sauyawa game da aurar da ‘yaya mata a kasar Hausa, amma kuma har yanzu akwai wasu wuraren da ke bin tsarin da addinin Musulunci ya shardanta cewa auren ‘ya mace budurwa, hakkin uba ne ya zaba mata mijin da zata aura, ba tare da saninta ko mahaifiyarta ba.

Alhaji Mai-Zabura ya ce abin da ya sa hakan yake faruwa saboda yawanci auren fari za ka ga ‘yan matan ba su mallaki hankalin da za su iya zabar mijin da ya dace da su ba, don haka iyaye ke zabar musu.

A wasu lokutan ma akan bayar da yarinya ga wanda ya kai sa’an mahaifinta, ko da kuwa ba ta so, musamman idan iyaye suka ga ta kara shekaru kuma babu wanda ya fito neman aurenta.

”Muna ganin idan ba mu yi sauri muka zaba wa ‘yayanmu mazajen aure ba, abin ya kan zama da matsala, ko kuma yarinya ta sangarce babu mai aurenta, shi ne abin fargaba,” in ji Mai-Zabura.

Hakan ba ya rasa nasaba da kananan shekarun da yarinya ke da shi da za a iya cewa ba ta mallakai hankalinta ba ta yadda za ta iya zabar abin da ya dace da ita, da kan sa auran fari iyaye ne ke da zabi.

Hajiya Amina ta ce tana da shekara 13 aka yi mata aure, kuma ba su taba ganin juna ita da mijin ba.

”Lokacin ina makarantar kwana, kakana ya zo ranar ziyara ya kawo min kayayyaki, daga nan ya saka hannu a aljihunsa ya dauko katin daurin aure yi mika min ya ce ‘ga shi nan na riga ya daura miki aure’, na kuma amsa na amince haka,” in ji Amina.

Amma kuma wasu iyayen sukan bar yarinya ta zabi wanda ta ke so bayan sun fahimci cewa zabinsu na farko bai yi tasiri ba.

Wasu masu lura da al’amuran zamantakewa na cewa a yanzu saboda zurfin karatu da galibi yaya mata ke yi, sukan kai shekarun da su kan fahimci abubuwan zamantakewar aure da mu’amala da jama’a, kuma yanayin auren na yanzu na soyayya ake yi ba na dole ko na zabin iyaye ba.

Rawar da wakokin rakiyar amarya ke takawa

A shekarun baya, ya zama wata al’ada da kuma nishadantarwa a lokacin da za a raka amarya gidan mijinta, ‘yan mata kawaye kan rika rera wakoki ga amaryar.

Galibi irin wadannan wakoki kan sosa ran amarya har ta rika rusa kuka.

Hajiya Fatima Haruna ta ce tabbas irin wadannan wakoki kan yi tasiri wajen saka amarya kuka a lokacin da za a raka ta gidan miji.

”Irin wadannan wakoki sukan tayar da hankalin amaryar da kuma fusata ta saboda kalaman da ke ciki na alhini da sosa rai, ta kan rika tunanin kamar ta rabu da iyayenta da ‘yanuwanta ne har abada, sai ta fashe da kuka,” in ji ta.

Ta ce ” Wakokin sun hada da kamar su:

Da na bi ki mun tafi tare

Ta kuma ce akwai waka kamar:

Duka irin wadannan wakoki kamar yadda Alhaji Mai-Zabura ya shaida wa BBC, kawayen amarya kan rika rera su ne lokacin da aka dora amarya a kan godiya ko kuma amalanke a wancan lokacin da dangi ‘yan rakiya da makada, don su kara tsokana da tsaoratar da amarya.

Ya ce: ”Hakan ke sa amarya hankalinta ya kara tashi ta fara kuka, tana ganin kamar za a kai ta inda ba za ta sake dawowa ba, kuma cikin wakokin akwai kalaman da ke nuna cewa rayuwar bam ai dadi ba ce, bauta ce da sauransu, shi ya ke sa kukan ai.”

Sai dai kuma sannu a hankali, duk da ba za a iya cewa an daina wannan al’ada ta kukan zuwa gidan miji ba a wannan zamani, amma kuma bayanai sun nuna cewa lamarin ya yi gagarumar sauyawa ba ma a cikin birane ba har ma da kauyuka.

Me ya sa al’amura suka sauya yanzu ba kamar zamanin da ba?

Idan aka kwatanta da yadda lamarin ke faruwa a zamanin yanzu ya sha bamban ba kadan ba a bisa wasu dalilai da ta bayyana na ci gaban da zamani ya zo da shi, kamar yadda Hajiya Amina Saulawa ta yi wa BBC karin bayani.

”Yanzu al’amura sun sauya, amma a wasu wuraren har yanzu ana samun ire-iren ‘yan matan da ke kuka idan za a kai su gidan miji,” in ji ta.

Amma kuma akwai bambanci tsakanin yadda hakan ke faruwa a wannan zamanin da kuma zamanin da, wato shekaru da dama da suka shude.

”Ai a zamanin da, ba a fada wa yarinya ko wane ne mijin da za a aurar mata, galibi auren gida ne ake yi, auren zumunci, yarinya ba za ta san mijinta ba sai ranar da aka kai ta. Tana dakin suruka nan take komai, sai ta kwana talatin ma bata ga mijin ba”, Mai-Zabura ya ce.

An fi dabbaka al’ada a lamarin aure a zamanin da ko kuma shekaru da dama da suka gabata, inda galibi akan yi wa ‘yan matan da basu wuce shekaru goma sha biyu ba ko ma kasa da haka aure.

Hausawa kan yi wata karin magana da su kan ce ”zamani riga”, saboda yadda wasu abubuwa sukan shude bayan wasu shekaru, a yayin da sabbi suka sha bamban da sukan shigo har su rika cin karo da su a al’adance.

Malama Fatima Haruna ta shaida wa BBC cewa ai su a lokacin da aka yi musu aure ba su ma san yadda gidan mijin ko kuma mijin yake ba, ba sa saka baki a cikin maganar bikin aure sai dai manya har a yi a gama.

”Yanzu babu irin wannan, budurwa ita ke yi wa kanta komai, ita ke zuwa ta duba gidan da za ta zauna, har ma a je a rika jera kayan daki da ita, a kai ta gidan miji, budurwa tana rabon katin aurenta,” in ji Fatima.

Yawan shekarun da ake kai wa ba a aurar da yarinya ba shi ma ya taka rawa wajen sauya al’amuran aure, da kuma rashin yin kuka idan za a kai yarinya gidan miji, in ji Mai-Zabura.

More News

APC ta dakatar da Ganduje a matakin gunduma

Mambobin jam'iyyar APC a mazabar da ke Karamar Hukumar Dawakin Tofa a Jihar Kano sun dakatar da Shugaban Jam’iyyar APC na kasa Abdullahi Ganduje. ...

Yadda rikici a kan gishirin N20 ya yi sanadiyyar mutuwar wani mutum a Kano

Wani magidanci mai suna Zakari Hamza mai shekaru 45, ya gamu da ajalinsa a hannun kanen matarsa, wani Magaji Salisu saboda gishirin N20. Dan marigayin,...

Sojoji Sun Kashe Mayaƙan IPOB 5

Dakarun rundunar sojan Najeriya da kuma ta rundunar sojan ruwan Najeriya a ranar Talata sun kashe mayaƙan ƙungiyar IPOB guda biyar a yayin musayar...

ÆŠan agajin Izala ya samu lambar yabo, kujerar hajji, kyautar mota bayan ya tsinci naira miliyan 100 ya mayar wa mai su

Salihu AbdulHadi Kankia, mamba ne na kungiyar agaji ta kungiyar Jama’atu Izalatil Bid’ah Wa Iqamatus Sunnah (JIBWIS), ya samu yabo da tukuicin mayar da...