Atiku Ya Ce Bai San Ko Zai Tsaya Takara A 2027 Ba

Tsohon Mataimakin Shugaban Kasa, Atiku Abubakar, ya bayyana cewa har yanzu bai yanke shawara ba kan ko zai tsaya takarar shugabancin kasa a shekarar 2027.

Atiku, wanda ya tsaya takara har sau shida a baya, ya bayyana haka ne a wata hira a wani shiri na talabijin mai suna Untold Stories, wanda Adesuwa Giwa-Osagie ke jagoranta.

Wannan bayani na Atiku na zuwa ne bayan da ya kaddamar da wani kawance na shugabannin jam’iyyun adawa da nufin kifar da gwamnatin jam’iyyar APC da Shugaba Bola Tinubu ke jagoranta.

Lokacin da aka tambaye shi ko zai sake tsayawa takara a 2027, Atiku ya ce: “Ban sani ba, domin dole ne a samu ingantaccen dandali na siyasa, musamman a wannan lokaci da kasar nan ke cikin mawuyacin hali tun bayan dawowar mulkin dimokuradiyya.”

Sai dai tsohon mataimakin shugaban kasar bai rufe kofar tsayawa takara ba, inda ya jaddada bukatar samun jagoranci mai kwarewa da cancanta a Najeriya.

More from this stream

Recomended