ASUU ta janye yajin aiki, an sake rufe makarantu a Najeriya

Yayin da muke shiga sabon mako kuma na ƙarshe a shekarar 2020, mun zaƙulo muku wasu daga cikin labaran da suka fi jan hankali a makon da muke bankwana da shi.

Litinin:- Gwamnatin Najeriya ta bayar da umarnin rufe makarantu da wuraren shaƙatawa

Kwamitin shugaban ƙasa da ke yaƙi da annobar korona, ya sake bayar da umarni ga ma’aikatan gwamnati daga mataki na 12 zuwa ƙasa da su zauna a gida har nan da makonni biyar.

A cewar kwamitin wanda ke ƙarƙashin jagorancin sakataren gwamnatin tarayya, Boss Mustapha, duka makarantu a faɗin ƙasar za su zama a rufe har zuwa watan Janairun 2021.

Kwamitin ya bayyana cewa gidajen rawa da wuraren shan barasa da kuma wuraren motsa jiki za su ci gaba da zama a rufe a ƙasar.

Kwamitin ya bayar da umarnin rufe gidajen abinci

Haka kuma gwamnatin ta saka takunkumi kan taruka irin na addini inda kwamitin ya ce ko wane wuri kada ya ɗauki sama da kashi 50 cikin 100 na mutanen da yake ɗauka a baya.

Gwamnatin ta kayyade tarukan addini su zama kasa da kashi 50 na inda wuraren ibada ke ɗauka, domin tabbatar da ba da tazara da kuma sanya takunkumi.

Boss Mustapa ya ce dukkan taron da za a yi ya wuce mutum 50 to a tabbatar da an yi shi a buɗaɗɗen waje mai makon a ɗakin taro.

Haka na ababan hawa su ɗauki kashi 50 na fasinjan da suke iya ɗauka domin bin dokar ba da tazara.

Ya ƙara da cewa an ɗauki bayanan matafiyan da suka shigo ƙasar daga waje su 163,818 kuma an wallafa a shafin gwamnatin.

Majalisar Dattawan Najeriya ta amince da kasafin kudin 2021

A wannan rana ne kuma majalisar Dattawan Najeriya ta amince da kasafin kudin 2021 a zamanta na musamman a yau Litinin.

Majaliar ta amince da naira tiriliyan 5.6 a matsayin kudin ayyukan yau da kullum da tiriliyan 4.1 na manyan ayyuka da tiriliyan 3.3 na biyan bashi.

Kazalika, an ware naira tiriliyan 4.1 a matsayin gudummawar da za a tattara domin gudanar da manyan ayyuka.

Jumilla, majalisa ta amince da kudi naira tiriliyan 13.5, karin biliyan biyar kenan a kan wanda Shugaba Buhari ya gabatar mata a watan Oktoba na tiriliyan 13.

Bayan kammala yi wa kasafin karatu na uku a yau, Shugaban Majalisa Ahmad Lawan ya nuna jin dadinsa kan yadda suka amince da kasafin kafin tafiya hutun Kirsimeti da sabuwar shekara.

“Bari na fara yi mana murnar yin aiki tukuru wurin ganin mun amince da kasafin 2021 a kan lokaci kafin tafiya hutun Kirsimeti,” in ji shi.

Tun farko Buhari ya gabatar da kunshin kasafin naira tiriliyan 13 (13,082,420,568,233), wanda ya zarta na 2020 da tiriliyan 2.28, inda na baran ya kasance naira tiriliyan 10.805.

Talata: Buhari ya sake tsawaita wa’adin kwamitin da ya kafa na yaƙi da korona

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari, ya sake tsawaita wa’adin kwamitin da ya kafa na yaƙi da annobar korona zuwa ƙarshen Maris ɗin 2021

A wani saƙo da shugaban ya wallafa a shafinsa na Twitter, ya ce ba zai yiwu ci gaban da aka samu na watanni tara da suka gabata ya tafi haka nan ba.

Shugaban ya ce “na tsaya na yi nazari kan lamarin kuma na aminta da cewa akwai buƙatar ɗaukar matakan gaggawa wajen daƙile yaɗuwar wannan cutar ta korona.

Shugaban ya kuma yi kira ga masu sarautun gargajiya da kuma malamai da su ba kwamitinsa haɗin kai wurin wayar da kan al’umma kan cutar.

A jiya ne dai kwamitin shugaban ƙasar da ke yaƙi da korona ya sake bayar da umarni ga ma’aikatan gwamnati daga mataki na 12 zuwa ƙasa da su zauna a gida har nan da makonni biyar.

Haka kuma kwamitin ya sanar da rufe duka makarantu da kuma wuraren motsa jiki.

Kwamitin kuma ya saka takunkumi kan taruka irin na addini inda kwamitin ya ce ko wane wuri kada ya ɗauki sama da kashi 50 cikin 100 na mutanen da yake ɗauka a baya.

Laraba:- ASUU ta janye yajin aikinta na tsawon wata tara a Najeriya

Ƙungiyar ta sanar da hakan ne a wani taron manema labarai da ta gudanar a ranar Laraba da safe.

Shugaban ASUU na ƙasa Biodun Ogunyemi ne ya sanar da hakan a yayin taron da suka yi a Abuja, inda ya yi ƙarin bayani kan yadda ƙungiyar ta cimma hakan.

ASUU ta bayyana cewa ta amince da tayin da gwamnatin tarayya ta yi mata ne shi ya sa ta amince da janyewa bayan tsawon wata tara.

An sha kai ruwa rana tsakanin gwamnatin Najeriya da ASUU kan batun janye wannan yajin aiki na sai Baba ta gani.

Ɗaliban Najeriya sun yi ta roƙon gwamnati a lokuta daban-daban a shafukan sada zumunta ta hanyar amfani da maudu’ai da dama duk don a janye yajin aikin su koma aji.

Alhamis:- An gano ma’aikatan bogi fiye da 25,000 a jihar Borno

Gwamnatin jihar borno da ke arewa maso gabashin Najeriya ta ce an gano ma’aikatan bogi 25,056 a jihar a matsayin malaman makaranta da ma’aikatan ƙananan hukumomi.

A wata sanarwa da ta aike wa manema labarai, gwamnatin ta ce an gano hakan ne bayan umarnin da Gwamna Babagana Umara Zulum ya bayar na yin binciken tantancewa har sau biyu.

Kwamitoci biyu na tantance ma’aikatan ƙananan hukumomi da na malaman makaranta ne suka gabatar da rahoton binciken nasu ga gwamnan.

Daga cikin jumullar ma’aikatan bogin, 14,762 suna karɓar albashi ne a matsayin ma’aikatan ƙananan hukumomi, yayin da 7,794 kuma malaman makaranta ne na bogi.

A sakamakon hakan sanarwar ta ce gwamnati ta yi nasarar samun rarar naira miliyan 420 kamar yadda bayanan da gwamna ya gabatar suka nuna.

Naira miliyan 183.6 an same su ne bayan dakatar da biyan ma’aikatan bogi na ƙananan hukkmomi yayin da aka samu naira miliyan 237 da ake biyan malaman makaranta.

Juma’a:- An bayar da belin matar da ake zargi da kashe ‘ya’yanta a Kano

An bayar da belin nata ne kan dalilan rashin lafiya amma duk da hakan kotu ta ce za a rinƙa kai ta asibitin masu taɓin hankali domin duba lafiyarta da sanar da kotu halin da take ciki.

Lamarin wanda ya faru tun a watan Oktoba a Unguwar Sagagi Layin ‘Yan Rariya a birnin Kano, da farko an bayyana cewa saɓani ne da mijinta saboda ya yi mata kishiya a watannin baya ya kai ga kisan ƴaƴansu.

Amma daga baya mahaifiyar matar da mijinta sun ce ta daɗe tana fama da rashin lafiya mai nasaba da iskokai kuma tana nuna alamun hakan.

Ta kuma shaida cewa tun da ta aurar da ƴarta shekara shida da suka gabata, ƴarta take tafka rikici da mijinta. “Kullum faɗa suke da mijinta,” in ji uwar matar.

A halin yanzu dai lauyoyin matar da ake zargin ne suka nemi belinta, kuma tana asibitin Aminu Kano a ɓangaren duba lafiyar ƙwaƙalwa.

Haka kuma za ta ci gaba da bayyana a gaban kotun majistare da ke Gidan Murtala.

Tun a lokacin da lamarin ya faru, BBC ta yi kokarin jin ta bakin mahaifin yaran da aka kashe ma’ana mijin matar da ake zargi da kashe ƴaƴan natan, amma bai iya magana ba saboda yanayi na juyayi da alhini da yake ciki sakamakon abin da ya faru.

Lamarin dai ya ɗauki hankulan jama’a da dama musamman ganin irin shaƙuwar da ke tsakanin ɗa da mahaifi, abin da wasu ke ganin ruwa ba ya tsami banza, kuma dalilin kishi ba zai sa uwa ta hallaka ƴaƴanta ba, don haka mutane ke fatan samun sahihiyar amsa bayan kammala shari’ar da ake yi mata.

Asabar:- Boko Haram ta kashe mutum 11 a Jihar Borno

Akalla mutum 11 ne suka mutu cikin wani hari da mayaƙan Boko Haram suka kai kan wani kauyen da galibin mazaunansa Kiristoci ne a Jihar Bornon Najeriya.

Kazalika, mayaƙan sun yi awon gaba da wani limamin Kirista da wasu mazauna kauyen Pemi a harin wanda suka kai ranar Alhamis, inda suka ƙona gine-gine da wata coci.

Ganau sun ce maharan sun shiga garin na jihar Borno ne cikin motoci da babura suna harbin kan mai tsautsayi yayin da mutane ke shirye-shiryen shagulgulan Kirsimati.

Wasu mazauna garin sun tsere zuwa cikin daji domin tsira da rayukannsu.

“‘Yan ta’addan sun kashe mutum bakwai, suka ƙona gida 10 sannan suka wawashe kayan abincin da ake shirin raba wa mutane domin bikin Kirsimeti,” kamar yadda wani ganau ya shaida wa AFP.

“Daga baya aka gano wasu gawarwakin guda huɗu a dajin da ke kusa da garin,” a cewar wani dattijo a yankin.

(BBC Hausa)

More News

EFCC na neman Yahaya Bello ruwa a jallo

Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arzikin Kasa Ta’annati (Economic and Financial Crimes Commission) ta bayyana tsohon gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello a matsayin...

Mutane da dama sun mutu bayan motar fasinja ta taka bam a Borno

Akalla mutane 16 ne ake fargabar sun mutu yayin da wasu 20 suka jikkata bayan wata motar fasinja da ke kan titin Baga-Kukawa a...

Sojoji Sun Ceto Lydia Simon Ɗaya Daga Cikin Ƴan Matan Chibok

Dakarun sojan Najeriya dake aiki da rundunar samar da tsaro ta Operation Desert Sanity III sun samu nasarar ceto, Lydia Simon ɗaya daga cikin...

Gwamna da ƴansanda sun daƙile yunkurin EFCC na kama Yahaya Bello

A ranar Laraba ne Gwamnan Jihar Kogi, Usman Ododo, ya dakile wani yunkurin da Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arzikin Kasa Ta’annati ta...