Arsenal ta guje wa abin kunya a Emirate | BBC Hausa

Pierre-Emerick Aubameyang
Hakkin mallakar hoto
@Arsenal
Image caption

Aubameyang ne ya ci kwallon nasarar

Kayataccen bugun tazara da Pierre-Emerick Aubameyang ya buga ne ya tabbatar wa da Arsenal nasara a Emirate bayan ta farke kwallo biyu da Aston Villa ta saka mata a raga.

Aubameyang ya cilla kwallonsa ta bakwai ne a raga ana saura minti shida a tashi daga wasan da suka kare shi da mutum 10 a fili bayan an kori Ainsley Maitland-Niles tun a minti na 41.

Villa sun shiga gaban Arsenal ne ta hannun John McGinn a minti na 20. Arsenal ta rama ta hannun finaretin sabon dan wasa Nicolas Pepe, wadda ita ce kwallonsa ta farko ga Gunners.

Kasa da minti biyu bayan haka Wesley ya sake saka Villa a gaba bayan Jack Grealish ya bugo masa kwallo a sama.

Saura minti tara a tashi daga wasa Calum Chambers ya farke wa Arsenal, kafin makararren harin da Aubameyang ya kai, wanda ya bai wa Gunners din nasararsu ta uku a Premier.

Hakan ya sa Arsenal ta dawo cikin ‘yan hudun farko da maki 11 a mataki na 4.

More News

EFCC na neman Yahaya Bello ruwa a jallo

Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arzikin Kasa Ta’annati (Economic and Financial Crimes Commission) ta bayyana tsohon gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello a matsayin...

Mutane da dama sun mutu bayan motar fasinja ta taka bam a Borno

Akalla mutane 16 ne ake fargabar sun mutu yayin da wasu 20 suka jikkata bayan wata motar fasinja da ke kan titin Baga-Kukawa a...

Sojoji Sun Ceto Lydia Simon ĆŠaya Daga Cikin Ćłan Matan Chibok

Dakarun sojan Najeriya dake aiki da rundunar samar da tsaro ta Operation Desert Sanity III sun samu nasarar ceto, Lydia Simon É—aya daga cikin...

Gwamna da ƴansanda sun daƙile yunkurin EFCC na kama Yahaya Bello

A ranar Laraba ne Gwamnan Jihar Kogi, Usman Ododo, ya dakile wani yunkurin da Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arzikin Kasa Ta’annati ta...