Annobar cutar kwalara ta kashe mutane 7 a Jigawa

An samu ɓarkewar annobar cutar kwalara a ƙaramar hukumar Kirikasamma da kewayenta a jihar Jigawa.

Kawo yanzu mutane 7 aka tabbatar da mutuwarsu sanadiyar annobar a yayin a wasu da dama ke can kwance a asibiti inda suke karbar magani.

Jami’in tsare-tsare na hukumar kula da lafiya a matakin farko na Æ™aramar hukumar Kirikasamma, Musa Abdullahi Digadige ya ce É“arkewar annobar cutar ta shafi Æ™auyuka da dama da suka haÉ—a da Malori, Maikintari, Dilmari, Kirikasamma, da kuma wani sashe na na Æ™auyen Baturiya.

A cewar Digadige alamomin cutar sun haɗa da gudawa,  ƙullewar ciki, jin yin amai, amai da kuma zazzaɓi.

Shugaban Sashen Ruwa da Tsafta, Muhammad Maisamari ya ce an tura tawagar jami’an kiwon lafiya ya zuwa yankunan da abun ya shafa domin su bayar da kulawar  da ta kamata.

Ƙaramar hukumar ta kuma sayo magunguna da sauran kayayyakin da suka kamata domin samun nasarar maganin cutar.

Daraktan mulki da gudanarwa na ƙaramar hukumar, Idris Gambo Abubakar ya yi alƙawarin bayar da dukkanin taimakon da ya dace domin daƙile yaɗuwar cutar.

Hukumomi sun alaƙanta ɓarkewar cutar da gurɓatar ruwan sha sanadiyar ambaliyar ruwa da aka samu a yankin sanadiyyar mamakon ruwan sama.

More News

Jam’iyar PDP ta dakatar da Dino Melaye

Jam'iyar PDP a jihar Kogi ta dakatar da Dino Melaye tsohon ɗantakarar gwamna a jihar kan zargin cin amanar jam'iya. Shugabannin jam'iyar PDP na mazaɓar...

Sojoji sun kashe gawurtaccen É—an bindiga Kachalla Buzu

Dakarun rundunar sojan Najeriya sun samu nasarar kashe gawurtaccen É—an bindiga Kachalla Halilu Sububu wanda aka fi sani da Kachalla Buzu. An kashe Kachalla ne...

Dakarun Najeriya sun hallaka Æ´anbindiga a Neja

Rundunar sojin saman Najeriya ta hakala 'yanbindiga sama da 28 a yankin ƙaramar hukumar Shiroro dake jihar Neja.Wata sanarwa da mataimakin daraktan yaɗa labarai...

Tinubu ya gana da Sarki Charles

Shugaban ƙasa, Bola Ahmad Tinubu ya samu kyakkyawar tarba daga Sarki Charles na Birtaniya a fadar Buckingham a wata ziyara da yakai. Wannan ce ganawa...