Annobar coronavirus ‘na iya gushewa cikin shekara biyu’ – Shugaban WHO

Tedros Adhanom Ghebreyesus (file photo)

Bayanan hoto,
Dr Tedros ya ce dunƙulewar duniya wuri guda ya taimaka wa kwayar cutar yaɗuwa cikin hanzari

Shugaban Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) ya ce yana fatan za a ga ƙarshen annobar korona nan da ƙasa da shekara biyu.

Yayin da yake jawabi a Geneva ranar Juma’a, Tedros Adhanom Ghebreyesus ya ce an shafe shekara biyu kafin aka dakile annobar murar nan ta Spanish flu ta shekarar 1918.

Amma ya Ć™ara da cewa ci gaban da aka samu a fagen fasahar zamani na iya ba duniya damar kawo Ć™arshen cutar “a Ć™anĆ™anin lokaci.”

“Saboda yadda sassan duniyarmu ke haÉ—e da juna, cutar ta sami damar bazuwa cikin sauĆ™i,” inji shi.

“Amma duk da haka muna da fasahar dakatar da cutar, da kuma ilimin dakatar da ita,” amma ya jaddada muhimmancin “haÉ—a kai na Ć™asa da Ć™asa”.

Annobar Spanish flu ta 1918 ta halaka a kalla mutum miliyan 50.

Kawo yanzu annobar korona ta kashe kusan mutum dubu 800 baya ga mutum miliyan 22.7 da suka kamu da cutar.

Dr Tedros ya amsa wata tambaya da aka yi ma sa kan rashawa kan batun samar da kayan samar wa ma’aikatan jinya kayan da ke kare su da kamuwa da cututtuka (PPE), wanda ya bayyana a matsayin “babban laifi”.

“Irin wannan babban laifi ne da a gani na daidai yake da laifin kisa. Sabooda ma’aikacin da ba shi da kayan kariya na PPE na cikin hadarin rasa ransa ne.

Duk da yake tambayar ta shafi Afirka ta Kudu ce, amma wasu Ć™asashen ma sun fuskanci irin wannan matsalar ta badaƙƙalar kayan samar da kariya ga ma’aikatan jinya.

Ranar Juma’a an yi wata zanga-zanga a Nairobi, babban birnin Ć™asar Kenya kan yadda wasu jami’ai suka mayar da annobar hanyar samun abin duniya, kuma likitoci a asibitocin gwamnati sun fara yajin aiki saboda rashin biyansu albashinsu da Ć™arancin kayan kariya.

Bayanan hoto,
An yi zanga-zanga a Nairobi ranar Juma’a

A Amurka, É—an takarar muĆ™amin shugaban Ć™asa a jam’iyyar Democrat Joe Biden ya caccaki Shugaba Trump kan yadda ya gaza magance matsalar annobar korona.

“Shugabanmu ya gaza bisa aikin da muka zabe shi ya yi. Ya gaza kare mu. Ya gaza kare Amurka,” inji Mista Biden.

An sanar da mutuwar fiye da mutum 1,000 a Amurka ranar Juma’a kawai, lamarin da ya kai yawan alĆ™aluman waÉ—anda suka mutu zuwa mutum 173,490.

[ad_2]

More News

EFCC na neman Yahaya Bello ruwa a jallo

Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arzikin Kasa Ta’annati (Economic and Financial Crimes Commission) ta bayyana tsohon gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello a matsayin...

Mutane da dama sun mutu bayan motar fasinja ta taka bam a Borno

Akalla mutane 16 ne ake fargabar sun mutu yayin da wasu 20 suka jikkata bayan wata motar fasinja da ke kan titin Baga-Kukawa a...

Sojoji Sun Ceto Lydia Simon ĆŠaya Daga Cikin Ćłan Matan Chibok

Dakarun sojan Najeriya dake aiki da rundunar samar da tsaro ta Operation Desert Sanity III sun samu nasarar ceto, Lydia Simon É—aya daga cikin...

Gwamna da ƴansanda sun daƙile yunkurin EFCC na kama Yahaya Bello

A ranar Laraba ne Gwamnan Jihar Kogi, Usman Ododo, ya dakile wani yunkurin da Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arzikin Kasa Ta’annati ta...