An yi zanga-zanga kan sanya haraji kan WhatsApp a Lebanon

A protester sits in front of flames in Dora, Lebanon

Hakkin mallakar hoto
Reuters

Image caption

Ana ci gaba da zanga-zanga a Lebanon duk da gwamnatin kasar ta janye kudurinta na kakaba haraji kan kiran waya ta manhajar WhatsApp.

Gwamnatin ta bayyana cewa za ta fara saka haraji na dala 0.20 a kowace rana kan kiran waya da aka yi da manhajar WhatsApp da kuma wasu manhajojin.

Amma ta janye wannan kudirin nata sa’o’i kadan bayan arangamar da aka samu tsakanin jami’an tsaro da kuma masu zanga-zanga.

An ruwaito cewa gwamman mutane ne suka samu raunuka a ranar Alhamis bayan masu zanga-zanga sun kona tayoyi jami’an tsaro kuma suka harba hayaki mai sa hawaye.

Hakkin mallakar hoto
Reuters

Image caption

Daya daga cikin masu zanga-zanga da karensa

Me ya sa mutane ke zanga-zanga a Lebanon?

Dubban mutane ne a kasar suka afka tituna a daidai lokacin da kasar ke fuskantar matsin tattalin arziki wanda ake zargin gwamnatin kasar da haddasawa.

Wani akanta daga cikin masu zanga-zangar a birnin Beirut ya shaida cewa ”Ina zaune a gida sai na ga mutane na zanga-zanga ni ma sai na bi su.

”Ina da aure akwai kudaden da ya kamata a bani duk wata wanda nake bin gwamnati amma ba a bani ba, ga shi bana aiki, laifin gwamnati ne.”

Hakkin mallakar hoto
EPA

More News

EFCC na neman Yahaya Bello ruwa a jallo

Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arzikin Kasa Ta’annati (Economic and Financial Crimes Commission) ta bayyana tsohon gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello a matsayin...

Mutane da dama sun mutu bayan motar fasinja ta taka bam a Borno

Akalla mutane 16 ne ake fargabar sun mutu yayin da wasu 20 suka jikkata bayan wata motar fasinja da ke kan titin Baga-Kukawa a...

Sojoji Sun Ceto Lydia Simon ĆŠaya Daga Cikin Ćłan Matan Chibok

Dakarun sojan Najeriya dake aiki da rundunar samar da tsaro ta Operation Desert Sanity III sun samu nasarar ceto, Lydia Simon É—aya daga cikin...

Gwamna da ƴansanda sun daƙile yunkurin EFCC na kama Yahaya Bello

A ranar Laraba ne Gwamnan Jihar Kogi, Usman Ododo, ya dakile wani yunkurin da Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arzikin Kasa Ta’annati ta...