An yi yunkurin juyin mulki a Ethiopia | BBC Hausa

Mr Abiy Ahmed

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Mista Abiy ya dauki matakan kawo karshen dambarwar siyasar kasar, ta Habasha, amma tashin hankali na kabilanci ya karu

Abiy Ahmed ya yi wannan sanarwar ne ta tashar talabijin din kasar, kuma abin mamaki a can cikin dare, yana sanye da kayan soji na rawar daji.

Ya ce wasu sojin haya sun kai hari kan hafsan hafsoshin sojin, amma kuma bai bayar da cikakken bayani kan halin da janar din yake ciki ba bayan da aka kai masa harin.

Mista Abiy ya kuma kara da cewa an hallaka wasu jami’an gwamnatin yankin na Amhara a lokacin wani zaman taro da abokan aikinsu.

Mazauna unguwar da ke kusa da hedikwatar ‘yan sandan, babban birnin yankin, na Amhara sun ce sun rika jin karar bundugogi ba kakkautawa a ranar Asabar da yamma a kusa da ginin.

Dga baya ma’aikatar harkokin waje ta Amurka ta fitar da wata sanarwa inda take gargadi ga ma’aikatanta a babban birnin kasar ta Ethiopia, Addis Ababa da kada su fito waje, inda sanarwar ke cewa ma’aikatar na sane da rahotannin musayar wuta a birnin.

Kafafen watsa labarai ma sun bayar da rahotannn cewa, wani yunkuri na hallaka gwamnanan yankin na Amhara, wanda ke biyayya ga Firaministan kasar, bai yi nasara ba.

Babu dai wani cikakken bayani game da yawan mutanen da yunkurin juyin mulkin ya rutsa da su.

Rahotanni sun ce tuni an baza dakarun gwamnatin tarayya a yankin, sannan kuma an ce an katse intanet a lokacin tsakar harin.

An dai zabo Mista Ahmed ne a shekarar da ta wuce domin ya kawo karshen dambarwar siyasar kasar ta Gabashin Afirka, inda ya saki fursunonin siyasa, ya cire haramcin da aka yi wa jam’iyyu tare da hukunta jami’an gwamnati da ake zargi da almundahana da cin zarafi.

sai dai kuma tun lokacin da ya kama mulki, an rikice-rikicen kabilanci sun kara tasowa, abin da ya kai ga mutane miliyan biyu da dubu 400 ‘yan kasar barin muhallansu, in ji Majalisar Dinkin Duniya

More News

Yahaya Bello Ya Bayyana Dalilan Da Ya Hana Shi Bayyana A Gaban Kotu

Tsohon gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello ya ce tsoron kamun  hukumar EFCC dake yaÆ™i da yiwa tattalin arzikin Æ™asa ne ya hana shi bayyana...

Ƴan sanda sun kama mutane biyu dake samarwa ƴan fashin daji makamai a jihar Kaduna

Rundunar Æ´an sandan jihar Kaduna ta ce tana tsare da wasu mutane biyu da ake zargi da safarar bindiga a jihar. A wata sanarwa ranar...

An kori sojojin Najeriya biyu saboda satar kebul a matatar Dangote

Rundunar sojin Najeriya ta tabbatar da korar wasu sojoji biyu da ake zargi da satar igiyoyin sulke a harabar matatar Dangote da ke jihar...

Magoya bayan APC da dama sun koma NNPP a Kano

Jam'iyar NNPP ta karɓi magoya bayan jam'iyar APC da dama a jihar Kano. Mataimakin gwamnan jihar Kano, Aminu Abdul Salam Gwarzo shi ne ya karɓi...