An yi garkuwa da mutane 40 a lokacin da suke ibada a coci

Akalla mutane 40 ne aka ruwaito a ranar Lahadin da ta gabata cewa wasu ‘yan bindiga sun yi garkuwa da su a yayin da suke gudanar da taro a cocin Bege Baptist dake Madala a karamar hukumar Chikun a jihar Kaduna.

Shugaban kungiyar Kiristoci ta Najeriya reshen jihar Kaduna, Rabaran John Hayab, ne ya bayyana lamarin a ranar Litinin.

A cewar Hayab, lamarin ya faru ne da karfe 9:30 na safe, a lokacin da ake gudanar da ibada.

An ambato shi yana cewa, “Masu ibadar suna cikin hidimar Lahadi a cikin Cocin sai da misalin karfe 9:30 na safe suka ji karar harbe-harbe a kusa da Cocin. ‘Yan bindigar sun kai hari Cocin kuma suka tafi tare da masu ibada 40.”

Sai dai ya kara da cewa 15 daga cikin masu ibadar da aka yi garkuwa da su sun yi nasarar tserewa, inda suka bar wasu 25 a maboyar masu garkuwar.

More from this stream

Recomended