‘An tafka magudi a zaben Kogi’ | BBC Hausa

Nigeria election worker marking ballots

A jihar Kogi da ke arewa ta tsakiyar Najeriya, ana ci gaba da dakon sakamakon zaben gwamna, wanda rikici ya dabaibaye.

Masu sa-ido kan zabe sun yi zargin cewa an yi magudi a zaben tare ta hanyar sayen kuri`a da firgita masu zabe, lamarin da ka iya shafar sahihancin sakamakon zaben.

A halin da ake ciki dai an kammala tattara sakamakon zaben a matakin gunduma da kananan hukumomi.

Hankali ya koma hedikwatar hukumar zabe ta kasa da ke Kogi don ganin yadda za ta hada alkaluma, kana ta sanar da sakamakon zaben gwamna, wanda aka kammala jiya.

Masu sa-ido a kan zaben da dama sun bayyana an samu yamutsi a rumfunan zabe a wasu yankuna jihar Kogi, musamman ma yadda ‘yan banga suka dinga cin karensu ba babbaka.

Sun dinga harba bindiga domin su tarwatsa jama’a, suna kuma fasa akwatunan zabe, suna kuma sace wasu.

A wata mazabar ma, irin Adankolo da ke gefen birnin Lokoja, mutum uku ne suka rasa rayukansu sakamakon harin da ‘yan bindiga suka kai, wadanda BBC ta tarar ana kokarin yi musu jana’iza.

Image caption

Natasha Akpoti, ‘yar takarar gwamnan Kogi a jam’iyyar SDP

Yaya masana siyasa ke kallon zaben?

Farfesa Jibrin Ibrahim, jami`i ne na cibiyar bunkasa demokuradiyya ta CDD da ke sa ido a kan zaben:

“Ana nun akarfin tuwo a wurare da yawa ko ma a hana zaben, a kori mutane, ko ma a kwashe kayan zaben.”

Ya kara da cewa: “Abin da fi ba mu maamki shi ne yadda aka bar ‘yan banga na yawo da motoci a cikin jihar ba tare da jami’an tsaro sun dauki mataki a kansu ba.”

Hukumar zaben Najeriya ta tabbatar da aukuwar wasu daga cikin aika-aikar, wasu kuma ta ce za ta bincika. Yayin da rundunar `yan sandan Najeriya ta ce jami`anta sun yi abin kirki, kasancewar sun kare kashi casa`in na jihar Kogin.

Ganin yadda rikici ya dabaibaye wannan zaben gwamnan, BBC ta tuntubi Alhaji Bala Salisu, wani jigo a jam`iyyar APC don jin ko za su rungumi kaddara su amince da duk yadda sakamakon zaben ya kasance?

“Babu wata kaddara da za mu runguma da ta wuce cewa wannan tafiya Allah Ya riga ya bai wa Bello.”

Shi ma Alhaji Baba Sule, jigo a jam`iyyar PDP cewa ya yi za su amince da sakamakon zaben, amma da sharadi:

“Idan aka bi tsari yadda doka ta ce, tabbas za mu amince da sakamakon zaben.”

Mutum 23 da uku ne suka takara kujerar gwamna a zaben, amma gwamna Yahaya Bello na jam`iyyar APC da Musa Wada na jam’iyyar PDP da kuma Natasha Akpoti ta jam’iyyar SDP su ne a sahun gaba.

More News

Majalisar dokokin jihar Kaduna ta nemi ma’aikatar kudin jihar ta miÆ™ata bayanan bashin da El-Rufai ya ciwo

Majalisar dokokin jihar Kaduna ta nemi ma'aikatar kudi ta jihar da ta miƙa mata cikakken bayani kan basukan  da gwamnatin tsohon gwamnan jihar, Nasiru...

An dakatar da ayyukan kamfanin jiragen sama na Dana Air

Festus Keyamo, ministan harkokin sufurin jiragen sama ya umarci hukumar FAAN dake lura da sufurin jiragen sama a Najeriya ta dakatar da ayyukan kamfanin...

Yahaya Bello Ya Bayyana Dalilan Da Ya Hana Shi Bayyana A Gaban Kotu

Tsohon gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello ya ce tsoron kamun  hukumar EFCC dake yaÆ™i da yiwa tattalin arzikin Æ™asa ne ya hana shi bayyana...

Ƴan sanda sun kama mutane biyu dake samarwa ƴan fashin daji makamai a jihar Kaduna

Rundunar Æ´an sandan jihar Kaduna ta ce tana tsare da wasu mutane biyu da ake zargi da safarar bindiga a jihar. A wata sanarwa ranar...