An Soke Zaben Fidda Gwani Na Jam’iyyar APC A Jihar Legas

Bayan da masu zabe suka shafe lokuta da dama suna zaben fidda gwani na gwamna a tutar APC a jihar Lagos, ‘yan kwamitin lura da zaben sunki amincewa da zaben tare da soke shi,kuma basu fadi ranar sake wani zaben ba, abinda magoya bayan wani dan takara ke zargin akwai lauje cikin nadi.

Shugaban kwamitin fidda gwanin takarar gwamna a jihar legas Mr. Clement Ebere ya bayyana soke zaben fidda gwanin dan takarar gwamna a jihar Legas inda yace kwamitin a shirye take da ta gudanar da zabe mai tsafta wanda zai samu amincewar kowane bangare daga cikun ‘yan takarar na jamiyyar APC.

Ya sjhaidawa yan jaridu cewa sun soke zaben ne domin kuwa har zuwa yammacin Talata basu samu cikakkun sunayen wakilan daya daga cikin ‘yan takarar da doka ta bada umarnin ace suna da shi ba, sai dai bai bayyana wanne daga cikin ‘yan takarar bane.

Zaben dai anayi tsakanin Babajide Olu ne dake samun goyon bayan shugaban jamiyyar ta APC Asiwaju Bola Tinubu da kuma gwamnan jihar Akinwome Ambode.

More News

Ƴan sanda sun kama mutane 6 da ake zargi da kisan kai da fashi da makami a Gombe

Rundunar ƴan sandan jihar Gombe ta ce a cikin mako guda  jami'an ta sun kama wasu mutane 6 da ake zargi da aikata fashi...

Ƴan sanda sun kama wani fursuna da ya tsere daga gidan Gyaran Hali na Maiduguri

Rundunar ƴan sandan jihar Borno ta ce jami'an ta sun kama Kyari Kur ɗaya daga cikin ɗaurarrun da suka tsere daga gidan gyaran hali ...

Ƴansanda sun kama mutumin da yake lalata da ƴar cikinsa

Jami’an rundunar ‘yan sandan jihar Ogun sun kama Ibrahim Aliu mai shekaru 41 a duniya a Papa Olosun, Oja Odan a karamar hukumar Yewa...

Majalisar wakilai za ta samar da jami’ar Bola Ahmad Tinubu

Ƙudurin kafa dokar kafa Jami'ar Karatun Yaruka Ta Bola Ahmad Tinubu ya tsallake karatun farko a majalisar wakilai ta tarayya. Mataimakin shugaban majalisar, Benjamin Kalu...