An samu dogayen layukan mai a Abuja da Lagos

Dogayen layukan mai sun sake bayyana a biranen Abuja da kuma Legas.

An ga  motoci a layukan mai a ranar Litinin inda suke jira su sha mai a wasu gidajen mai a yayin da wasu gidajen man suke a rufe..

Akwai dogon layin a gidan mai na kamfanin NNPCL dake kusa da hedkwatar cocin Dunamis.

Haka ma abun yake a gidan mai na Total Energies dake unguwar Lugbe.

Gidajen man Shema da NNPCL dake kan titin Karu dukkansu na rufe.

A birnin Lagos ma an ga dogayen layuka a wasu gidajen mai da suke da man a birnin.

Da yake magana kan halin da ake ciki, Clement Isong  sakataren kungiyar MEMAN ta  manyan dillalan makamashi ta Najeriya ya faɗawa Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya NAN cewa jinkiri da aka samu wajen ɗauko man daga depo shi ne musabbabin ƙarancin man.

More News

An gano gawarwakin ƴan fashin daji 8 a Kaduna

Gawarwaki 8 da ake zargin na ƴan fashin daji ne aka gano bayan da sojoji suka kai farmaki dazukan dake ƙauyen Kurutu dake kusa...

Tinubu ya karɓi Anyim Pius a jam’iyar APC

Shugaban ƙasa Bola Ahmad Tinubu ya yi wa  tsohon shugaban majalisar dattawa,Anyim Pius Anyim maraba da zuwa  jam'iyar APC. A makon daya gabata ne Anyim...

Akpabio ya bawa Natasha Akpoti hakuri

Shugaban majalisar dattawa, Sanata Godswill Akpabio ya bawa Sanata Natasha Akpoti daga jihar Kogi haƙuri kan furucin da ya yi mata akan gidan rawar...

Akpabio ya bawa Natasha Akpoti hakuri

Shugaban majalisar dattawa, Sanata Godswill Akpabio ya bawa Sanata Natasha Akpoti daga jihar Kogi haƙuri kan furucin da ya yi mata akan gidan rawar...