An samu bankin Musulunci a karo na biyu a Najeriya

Wani rahoton da muka samu a jiya Litinin daga jaridar Iwitness ta tabbatar da cewa babban bankin Nijeriya, CBN ta bayar da lasisin fara aiki ga wani sabon bankin Musulunci a Nijeriya, mai suna TAJ Bank Limited.

Majiyar mu ta ruwaito babban bankin ta sanar da amincewarta da fara aikin wannan sabon bankin Musuluncin ta cika ne cikin wata wasika data aika mata a ranar Litinin, 15 ga watan Yuli, sakamakon gamsuwa da tayi da cikan dukkan sharuddan data gindaya mata.

Sai dai CBN ta iyakance ayyukan Bankin TAJ a iya yankunan Arewa maso yammaci da kuma Arewa maso gabashin Najeriya, amma ta bata daman ta samar da babban ofishinta a babban birnin tarayya Abuja.

Wannan cigaba da aka samu a harkar cinikayyar kasuwanci irin na Musulunci ya kawo adadin bankunan Musulunci a Najeriya zuwa biyu, bayan samuwar bankin Musulunci na Jaiz tun a shekarar 2011.

Idan za’a tun a shekarar 2003 aka fara haihuwar Jaiz a matsayin cibiyar hada hada cinikayya irin na Musulunci da bata ta’ammali da riba, yayin da a shekarar 2011 CBN ta batalasisin fara aiki a iya Arewacin Najeriya, don haka ta zama bankin Musulunci na farko a Najeriya.

Bankin Musulunci na JAIZ bai fara aiki ba sai a ranar 6 ga watan Janairu na shekarar 2012, inda bayan samun karbuwa suka nemi izinin CBN ta basu daman su fadada ayyukansu zuwa sauran sassan Najeriya, wanda a shekarar 2016 CBN ta bata lasisin aiki a dukkanin sassan Najeriya.

More News

ÆŠalibai a Jami’ar Jos na zanga-zanga saboda rashin wuta da ruwa

Wasu daliban jami’ar Jos da ke jihar Filato a ranar Alhamis sun gudanar da zanga-zangar nuna rashin amincewarsu da matsalar karancin ruwa da rashin...

MTN yana ƙoƙarin ƙara kuɗin kati da data a Najeriya

Katafaren kamfanin sadarwa na MTN na kokarin kara kudin katin waya da na data a Najeriya. Kamfanin sadarwa mafi girma a nahiyar Afirka ya ba...

Gwamnatin Kano Ta Rage ₦500,000 A Kuɗin Aikin Hajjin Bana

Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf ya sanar da yiwa maniyatan Aikin Hajji da suka fito daga jihar kyautar ₦500,000 domin su cika kuɗin...

Ƴan bindiga sun sace wani limami a jihar Kogi

Ƴan bindiga sun yi garkuwa da Quasim Musa babban limamin garin Iyara dake ƙaramar hukumar Ijumu ta jihar Kogi. Lamarin ya faru ne a ranar...