Gwamnatin Najeriya ta saka jiragen shugaban ƙasa guda uku a kasuwa a wani yunkuri da mahukunta suka bayyana da cewa zai rage yawan kuɗaɗen da ake kashewa wajen kula da jiragen.
Hakan na zuwa ne a yayin da kwamitin majalisar wakilai kan tsaron ƙasa da kuma bayanan sirri ya bada shawarar sayen aƙalla jirage biyu domin amfanin shugaban ƙasar da kuma mataimakinsa.
Shehu Umar Buba, shugaban kwamitin majalisar dattawa kan tsaron ƙasa da kuma bayanan sirri ya goyi bayan matakin shawarar da kwamitin majalisar wakilan ya bayar.
Sayar da jiragen zai rage yawan jiragen shugaban ƙasar ya zuwa rabin adadin su.
A yanzu rukunin jiragen shugaban ƙasar na ɗauke da yawan jirage shida.
Tuni gwamnatin tarayya ta naɗa kamfanin JetHQ dake ƙasar Amurika a matsayin kamfanin da zai yi dillancin jiragen.