An kwaso yan Najeriya 161 daga Libiya bayan zaman gidan yari

Gwamnatin tarayya ta ce ofishin jakadancin Najeriya dake Libiya ya kwaso yan Najeriya 161 da suka aikata laifukan shige da fice na kasar.

Kabiru Musa jami’in dake lura da ayyukan ofishin jakadancin Najeriya a Libiya ne ya bayyana haka.

Mutanen da aka kwaso sun sauka a filin jirgin sama na Murtala Muhammed dake Lagos a ranar Litinin da daddare.

Ya ce an sake su ne daga gidan yari domin basu damar sake gina rayuwar su a gida Najeriya.

Ofishin jakadancin Najeriya dake Libiya tare da haɗin gwiwar hukumomin kasar da kuma hukumar Kula da Yan Gudun Hijira ta Majalisar Dinkin Duniya ne suka samu nasarar fito da mutanen daga gidan yari.

More from this stream

Recomended