An kwantar da shugaban NLC a asibiti bayan ya samu rauni a idonsa

Daga Sabiu Abdullahi

A halin yanzu dai ƙwararrun likitoci a asibitin koyarwa na jami’ar tarayya dake Owerri na kokarin ceto idanun Joe Ajaero, shugaban kungiyar kwadago ta Najeriya NLC, biyo bayan wani hari da aka yi musu a yayin wata zanga-zanga a jihar Imo ranar Laraba.

Rahotanni sun ce rundunar ‘yan sandan jihar Imo ta kama Ajaero a lokacin da yake jagorantar wata zanga-zanga, amma rundunar ta bayyana cewa an kubutar da shi daga hannun wasu gungun mutane ne.

Wani faifan bidiyo ya nuna yadda aka garzaya da Ajaero cibiyar kula da lafiya ta tarayya da ke Owerri a zaune a tsakanin wasu mutane biyu.

A cikin bidiyon, ya bayyana cewa ba shi da waya tare da shi amma yana fatar samun taimako daga wani dan uwan da ke aiki a FUTHO.

Jami’an NLC sun yi Allah wadai da lamarin, inda suka bayyana shi a matsayin wani yunkuri na sace mutane wanda ya rikide zuwa yunkurin kisan kai.

More from this stream

Recomended