An kubutar da wani fasto daga Boko Haram | VOA Hausa

Wadannan mutane sun hada ne da limamin wani cocin Living Faith Church dake a Maiduguri, Fasto Moses Oyeleke da wani dan uwansa da aka yi garkuwa da su watanni bakwai da suka gabata, yayin da suke hanyar su zuwa garin Chibok, a dai dai lokacin da suka isa garin Bama kafin su shiga Chibok.

Fasto Moses Oyeleke da aka kubutar da shi a ranar Lahadi, yace har yanzu dan uwansa na nan a hannun mutanen da suka yi garkuwa da su. Fasto Moses yace ya yi matukar farin ciki da ya dawo gida. Sai dai ya kara da cewa babu wata azaba da aka gana masa yayin da yake hannun wadanda suka yi garkuwa da shi.

Da yake zantawa da wakilin Muryar Amurka a Maiduguri, Fasto Moses Oyeleke yace masu garkuwa da shi sun nemi ya musulunta ya bar addininsa amma kuma ba tare da wata tsangwama ba, ya kuma ce sun yi zaman lafaiya da shi a tsawon lokaci da ya kwashe a wurinsu.

Wata yarin ‘yar shekaru 14 da kungiyoyi masu zaman kansu suka kubutar da ita bayan an sace ta a gidansu dake wani kauye a cikin karamar hukumar Askira Wuba dake kudancin jihar Borno, mai suna Jagilaye Ibrahim, ta bayyanawa Muryar Amurka irin hali da fada a ciki a hannun ‘yan Boko Haram.

Jagilaye Ibrahim, tace ta kwashe watanni tara a hannun masu garkuwa da ita ta kuma ga ana tursasa da wasu ‘yan mata da su kuma ake garkuwa da su ana aurar da su, sai dai tace ba a yi mata irin wannan auren ba.

More News

EFCC na neman Yahaya Bello ruwa a jallo

Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arzikin Kasa Ta’annati (Economic and Financial Crimes Commission) ta bayyana tsohon gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello a matsayin...

Mutane da dama sun mutu bayan motar fasinja ta taka bam a Borno

Akalla mutane 16 ne ake fargabar sun mutu yayin da wasu 20 suka jikkata bayan wata motar fasinja da ke kan titin Baga-Kukawa a...

Sojoji Sun Ceto Lydia Simon Ɗaya Daga Cikin Ƴan Matan Chibok

Dakarun sojan Najeriya dake aiki da rundunar samar da tsaro ta Operation Desert Sanity III sun samu nasarar ceto, Lydia Simon ɗaya daga cikin...

Gwamna da ƴansanda sun daƙile yunkurin EFCC na kama Yahaya Bello

A ranar Laraba ne Gwamnan Jihar Kogi, Usman Ododo, ya dakile wani yunkurin da Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arzikin Kasa Ta’annati ta...