An Kuɓutar Da Yara Arewa Da Aka Sayar A Kudancin Najeriya 

Cin zarafin da ake yi wa mutane na daga cikin matsalolin da ke ci gaba da dabaibaye Najeriya duk da fafutukar da hukumomi da kungiyoyi ke yi na yaki da matsalar.

Sau da yawa mahukunta suna kamawa tare da ceto mutanen da ke fadawa tarkon masu safarar bil’adama a sassa dabam-daban na Najeriya, kuma har yanzu matsalar ta ki karewa.

Jami’an tsaron hukumar DSS ta Najeriya sun samu nasarar ceto wasu yara hudu da aka sace daga arewacin kasar aka sayar da su a yankin kudu ga wasu iyalai bayan shekara biyu. Uku daga cikin yaran daga jihar Sokoto suka fito daya kuma daga jihar Kebbi duk a arewa maso yammacin Najeriya.

Jami’an tsaron na DSS sun danka yaran ga hukumar yaki da safarar bil’adama ta NAPTIP mai kula da shiyar Sokoto, Kebbi da Zamfara.

Barista Abubakar Bashiru, Shi ne jami’in gudanarwa na hukumar, ya tabbatar da ceto yaran ya kuma bayyana cewa a iya bincikensu sun kasa gano iyayen uku daga cikin yaran amma suna kan bincike. A halin yanzu dai ana tuhumar mutane 9 da ke hannun hukuma akan batun, a cewarsa.

Hukumar ta NAPTIP ita ma ta mika yaran ga gwamnatin jihar Sokoto kafin ta kammala bincikenta. Mashawarciyar gwamnan jihar Sokoto a fanni kare hakkokin bil’adama, Ubaida Bello, ta ce gwamnati ta karbe su kuma an sama musu wurin zama da masu kula da su har zuwa lokacin da za a gano iyayensu.

Kungiyoyin da ke fafutuka akan kula da kare hakkokin mata da kananan yara na ci gaba da nuna damuwa akan yadda har yanzu ana samun irin wadannan matsalolin a Najeriya.

A shekarun baya, an yi ta samun rahotannin sata da kuma sayar da kananan yara musamman a kudancin Najeriya. Matsalar yanzu ta fara bazuwa zuwa arewacin kasar abindayasa kungiyoyi masu fafutuka ke ci gaba da jan hankalin iyaye da su kara kula da ‘ya’yansu.

More News

MTN yana ƙoƙarin ƙara kuɗin kati da data a Najeriya

Katafaren kamfanin sadarwa na MTN na kokarin kara kudin katin waya da na data a Najeriya. Kamfanin sadarwa mafi girma a nahiyar Afirka ya ba...

Gwamnatin Kano Ta Rage ₦500,000 A Kuɗin Aikin Hajjin Bana

Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf ya sanar da yiwa maniyatan Aikin Hajji da suka fito daga jihar kyautar ₦500,000 domin su cika kuɗin...

Ƴan bindiga sun sace wani limami a jihar Kogi

Ƴan bindiga sun yi garkuwa da Quasim Musa babban limamin garin Iyara dake ƙaramar hukumar Ijumu ta jihar Kogi. Lamarin ya faru ne a ranar...

Delta: An dawo da gawarwakin sojojin da aka kashe Abuja don yi musu jana’iza

Gawarwakin sojojin da aka kashe a jihar Delta kwanan nan sun isa maƙabartar sojoji ta kasa da ke Abuja. Gawarwakin sun iso ne da misalin...