Wani jirgi marar tuki dake dauke da makami ya kashe sojojin kasar Amurka su 3 a wani sansaninsu dake kasar Jordan.
Ƙarin wasu sojoji 30 ne suka jikkata a harin da wata kungiyar fafutuka dake kasar Iraq ta kai.
Akwai kungiyoyi da dama dake adawa da kasar Isra’ila da kuma Amurka kasashen Iraqi, Syria, Yemen da kuma Lebanon dake samun goyon bayan kasar Iran.
Tuni kasar Iran ta musanta cewa tana da hannu a harin da aka kai kan sojan na Amurka.
Kungiyar da ta dauki alhakin kai harin ta ce zata cigaba da kai makamancin sa matukar Isra’ila bata daina kai hare-hare yankin Gaza ba.