An kamo kurar da ta tsere a jihar Filato

An kamo wata kura da ta tsere daga gidan ajiye namun daji dake Jos inda aka mayar da ita inda take.

An shiga zaman zullumi da tsoro a birnin na Jos a ranar Litinin bayan da aka samu rahoton tserewar kurar daga gidan ajiye namun daji dake Dong a ƙaramar hukumar Jos North.

A wata sanarwa ranar Talata,Chuwang Pwajok shugaban hukumar yawon buɗe ido ta jihar Filato ya ce an gano kurar ne bayan an ɗauki lokaci ana nemanta.

Pwajok ya godewa jama’a kan yadda suka kwantar da hankali da kuma bayar da haɗin kai da suka yi wajen neman kurar.

More News

An gano gawarwakin ƴan fashin daji 8 a Kaduna

Gawarwaki 8 da ake zargin na ƴan fashin daji ne aka gano bayan da sojoji suka kai farmaki dazukan dake ƙauyen Kurutu dake kusa...

Tinubu ya karɓi Anyim Pius a jam’iyar APC

Shugaban ƙasa Bola Ahmad Tinubu ya yi wa  tsohon shugaban majalisar dattawa,Anyim Pius Anyim maraba da zuwa  jam'iyar APC. A makon daya gabata ne Anyim...

Akpabio ya bawa Natasha Akpoti hakuri

Shugaban majalisar dattawa, Sanata Godswill Akpabio ya bawa Sanata Natasha Akpoti daga jihar Kogi haƙuri kan furucin da ya yi mata akan gidan rawar...

Akpabio ya bawa Natasha Akpoti hakuri

Shugaban majalisar dattawa, Sanata Godswill Akpabio ya bawa Sanata Natasha Akpoti daga jihar Kogi haƙuri kan furucin da ya yi mata akan gidan rawar...