An kama mutum biyu saboda kwarmata tambayar jarabawa | BBC Hausa

Dalibai a dakin jarabawa

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Dalibai a lokacin da suke rubuta jarabawa

‘Yan sanda na gudanar da bincike kan kwarmata tambayoyin jarabawar Lissafi ta makarantar gaba da Sakandare tare da cafke mutane biyu da ake zargi.

A ranar Litinin ne ‘yan sandan suka kama mutanen biyu da ake zargi da kwarmata tambayoyin, mace ‘yar shekara 29 da namiji dan shekara 32.

Bayan yi musu tambayoyi ‘yan sanda sun sallame su tare da ci gaba da sanya musu ido yayin da ake ci gaba da gudanar da bincike.

An dai wallafa tambayoyi biyu na jarabawar lissafi a shafin Twitter, wadda aka rubuta a ranar 14 ga watan Yuni.

Sannan a kasan tambayoyin aka bukaci daliban da suke da sha’awar sanin sauran tambayoyin su biya fan din Ingila 70, kwatankwacin Naira 32,000.

Tuni dai aka goge wannan bayanin daga shafin Twitter.

Shugaban makarantar da aka rubuta jarabawar ya ce ya san burin duk wani dalibi shi ne ya samu sakamakon jarabawa mai kyau, to amma ba ta barauniyar hanya ba.

A dan tsakanin nan batun satar jarabawa da kwarmata tambayoyin jarabawar gabannin yin ta na ci gaba da zama batun da ke ciwa hukumomin kasashen da ke fama da matsalar tuwo a kwarya.

Ko a farkon watannan kasar Habasha sai dai ta toshe internet a wasu sassan kasar da dalibai ke rubuta jarabawa duk domin kaucewa satar amsa.

More News

ÆŠalibai a Jami’ar Jos na zanga-zanga saboda rashin wuta da ruwa

Wasu daliban jami’ar Jos da ke jihar Filato a ranar Alhamis sun gudanar da zanga-zangar nuna rashin amincewarsu da matsalar karancin ruwa da rashin...

MTN yana ƙoƙarin ƙara kuɗin kati da data a Najeriya

Katafaren kamfanin sadarwa na MTN na kokarin kara kudin katin waya da na data a Najeriya. Kamfanin sadarwa mafi girma a nahiyar Afirka ya ba...

Gwamnatin Kano Ta Rage ₦500,000 A Kuɗin Aikin Hajjin Bana

Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf ya sanar da yiwa maniyatan Aikin Hajji da suka fito daga jihar kyautar ₦500,000 domin su cika kuɗin...

Ƴan bindiga sun sace wani limami a jihar Kogi

Ƴan bindiga sun yi garkuwa da Quasim Musa babban limamin garin Iyara dake ƙaramar hukumar Ijumu ta jihar Kogi. Lamarin ya faru ne a ranar...