An kama Hudu Ari kwamishinan zaben Adamawa

Ƴan sanda sun kama Barista Hudu Yunusa-Ari, kwamishinan zabe na jihar Adamawa, wanda aka dakatar saboda sanar da sakamakon zaɓen jihar ba bisa ka’ida ba.

Jami’in hulda da jama’a na rundunar ƴan sandan jihar, Muyiwa Adejobi, shi ne ya tabbatar da hakan a ranar Talata.

Ya ce kuma ana binciken wasu daga cikin mutanen da suka taka rawa a cece-kucen da Ari ya haifar.

Yunusa-Ari dai ya janyo ce-ce-ku-ce ne bayan da ya ayyana Sanata Aisha Dahiru, wanda aka fi sani da Binani, ta jam’iyyar APC a matsayin wadda ta lashe zaben a lokacin da ba a kammala tattara sakamakon zaben ba.

More from this stream

Recomended