Wasu mutane da dama sun gudanar da zanga-zanga a sassa daban-daban na birnin Lagos dama wasu birane a Najeriya.
Zanga-zangar cigaba ce ta zanga-zangar da aka gudanar a cikin watan Agusta domin nuna adawa da matsin rayuwa da ake fama a Najeriya.
Duk da gargadi da suka fuskanta daga jami’an tsaro kan kada a gudanar da zanga-zangar sai gashi mutane sun bazama kan tituna.
Mutane da dama a wurin zanga-zangar sun bayyana damuwarsu kan tsadar rayuwa da ake fama da ita musamman ta kayan abinci da suke nema su gagari da yawa daga cikin Æ´an Najeriya.
Wasu daga cikin allunan da masu zanga-zanga ke É—auke sun yi kira ga gwamnati da ta dawo da tallafin man fetur da kuma na wutar lantarki.