An gano kaburburan da masu sace jama’a suke binne mutane a Benue

An hako kaburbura da ake zargin an binne mutane a cikinsu

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

An hako kaburbura da ake zargin an binne mutane a cikinsu

Rundunar ‘yan sanda a jihar Binuwai da ke Najeriya ta ce ta hako wasu kaburbura da ake zargin an binne mutane a cikinsu.

Ana zargin kaburburan na wasu mutane ne da masu satar jama’a don neman kudin fansa suka kashe.

An gano kaburburan sakamakon kamen da ‘yan sanda suka yi wa wani wanda ya shaida wa jami’an cewa ya kashe wani, lamarin da ya sa ‘yan sandan suka je don gudanar da karin bincike.

Kwamishinan ‘yan sandan jihar, Muhammad Mukaddas ya shaida wa BBC cewa zuwa yanzu, sun damke mutane 7 wadanda a baya suka yi kaurin suna a fashi da makami yanzu kuma suke sace jama’a.

Ya ce wadanda ake zargin suna amfani da igiya wajen shake mutum har sai ya mutu sai kuma a cewarshi, su tona rami a gonaki sannan su binne su a ciki.

”Wasu ma har sun yi shuka a wajen domin boye aika-aikar da suke tafkawa, idan ba ka sani ba, za ka zaci doya ce ko rogo” in ji Kwamishinan ‘yan sandan.

Kwamishina Mukaddas ya ce sun gano wasu ramummuka a gonaki da aka binne mutane 16 a cikinsu sai dai ya musanta zargin da ake na cewa an samu wani kabari guda daya da aka binne mutane 16 a cikinsa.

Ya kara da cewa bincikensu ya gano cewa daya daga cikin mutanen da suka shiga hannu yana zaune ne da iyalinsa a kusa da wajen ta’asar.

Mukaddas ya kare rundunar ‘yan sandan kan dalilin da ya sa sai a yanzu ne suka iya gano wannan maboya inda ya ce ”wajen yana da nisa daga titi sannan akwai duwatsu manya-manya da mutanen su ke amfani da su a matsayin maboya.”

Hakkin mallakar hoto
Google

Image caption

Muhammad Mukaddas Kwamishinan ‘yan sandan Jihar Binuwai

Kwamishinan ‘yan sandan ya ba da tabbacin gurfanar da mutanen gaban kotu duk da ya bayyana cewa binciken zai dauki dan lokaci kuma a cewarshi, za su ci gaba da kokarin lalubo sauran da suke aikata irin wannan ta’asar domin su girbi abin da suka shuka.

Jihar Binuwai da ke tsakiyar arewacin Nijeriya na daya daga cikin jihohin da ke fama da matsalolin tsaro ciki har da ayyukan fashi da makami da sauran rikice-rikice.

More from this stream

Recomended