An fitar da hotunan yadda ruwa ya tunkuɗo gawarwakin yaran bakin tekun Libiya

A man is rescued in the Mediterranean by an NGO, November 2017
Bayanan Majalisar Dinkin Duniya sun ce mutum 630 ne aka yi amannar cewa sun mutu a oárin tsalla Bahar Rum a bana kawai

Hukumar bayar da agaji ta Sifaniya ta rarraba hotunan gawarwakin yara da mata da ruwa ya koro bakin tekun Libiya.

Ƙungiyar ta Proactiva Open Arms ta samu wasu hotunan ne daga cikin Libiya ta kuma ce na mutanen da suka yi ƙoƙarin tsallake Bahar Rum zuwa Turai, ta wata hanya mai haɗari da ƴan ci rani ke bi.

Hotunan sun nuna gawarwakin ƙananan yara da mata da babu isasshiyar sutura a jikinsu, yadda suka kumbura sannan ƙasa ta turbuɗe su.

A ƙalla ƴan ci rani 743 ne suka mutu a Bahar Rum a wannan shekarar.

“Muna cikin kaɗuwa,” kamar yadda shugabar sashen sadarwa ta Open Arms Laura Lanuza ta shaida wa BBC.

“A yayin da mutane suka yi ƙoƙarin tserewa daga Libiya ba za a mayar da su ko a bar su cikin halin ni ƴasu a Bahar Rum ba. Dole a yi aikin nemansu da cetonsu… don kare rayuka a teku.”

“Bahar Rum ce babbar maƙabarta mafi girma a duniya, wato inda mutane suka fi mutuwa,” a cewarta. Bai kamata ya kasance haka ba.”

Da yake mayar da martani a kan hotunan, Firaiministan Italiya Mario Draghi ya ce: “Hotunan gawarwakin yara da jarirai da ruwa ya tunkuɗ bakin teku ba abin yarda ba ne.”

Ɗaya daga cikin hotunan da aka yaɗa a intanet ya nuna yadda wani ƙaramin yaro sanye da wata yagalgalalliyar rigar barci. Ƙasa ta rufe gawar tasa.

Wani hoton kuma na wata mace ce sanye da koren dogon wando kwance ɗaiɗai a ƙasa, rigarta ta zame daga jikinta.

Oscar Camps shi ne wanda ya ƙirƙiri Proactiva Open Arms. Ya wallafa hotunan gawarwakin yara ƙanana da mata a Tuwita a ranar Litinin, waɗanda ke cike da fatan cikar burikansu,” yana mai cewa an bar gawarwakin a wajen har tsawon kwana uku.

Wata ƴar jarida Nancy Porsia – wadda ita ma ta wallafa hotunan gawarwakin a intanet – ta wallafa cewa wani da ta sani ne ya ga gawarwakin a ranar Asabar ya kuma sanar da hukumomi, waɗanda suka binne su a ranar a maƙabartar Abu Qamash.

Turai na ta fama da tururuwar ƴan ci rani da ke neman shiga yankin ta hanyar tsallake Tekun Bahar Rum. A bana tuni mutum 13,000 suka isa Italiya, sannan zafin ranar da ake fama da shi na iya sanya wa wasu mutanen masu yawa su ƙara ƙoƙarin tsallake Bahar Rum ɗin.

Sannan a yammacin Bahar Rum ɗin a makon da ya gabata , wasu mutum 8,000 da suka haɗa da yara da suka yi ta ninƙaya ko yin rara-gefe ta jikin katangar kan iyaka don shiga Sifaniya daga Moroko. Daga baya hukumomi sun mayar da dubbai ba tare da ɓata lokaci ba.

A shekarar 2015, hoton wani yaro da ya nutse mai suna Aylan Kurdi ya jawo ce-ce-ku-ce a duniya. An ɗauki hoton yaron ne ɗan ƙasar Syria wanda ke kwance ruf da ciki a ƙasa a Turkiyya bayan da iyalansa suka yi ƙoƙarin isa Turai.

More News

EFCC na neman Yahaya Bello ruwa a jallo

Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arzikin Kasa Ta’annati (Economic and Financial Crimes Commission) ta bayyana tsohon gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello a matsayin...

Mutane da dama sun mutu bayan motar fasinja ta taka bam a Borno

Akalla mutane 16 ne ake fargabar sun mutu yayin da wasu 20 suka jikkata bayan wata motar fasinja da ke kan titin Baga-Kukawa a...

Sojoji Sun Ceto Lydia Simon Ɗaya Daga Cikin Ƴan Matan Chibok

Dakarun sojan Najeriya dake aiki da rundunar samar da tsaro ta Operation Desert Sanity III sun samu nasarar ceto, Lydia Simon ɗaya daga cikin...

Gwamna da ƴansanda sun daƙile yunkurin EFCC na kama Yahaya Bello

A ranar Laraba ne Gwamnan Jihar Kogi, Usman Ododo, ya dakile wani yunkurin da Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arzikin Kasa Ta’annati ta...