An dakatar da ma’aikatan gwamnati 500 a jihar Adamawa

Fintiri

Gwamnatin jihar Adamawa ta dakatar da wasu ma`aikatan Kwalejin fasahar jihar kusan mutum 500 daga aiki.

Gwamnatin dai ta ce ta sallame su ne saboda ba a bi ka`ida ba wajen daukarsu aiki.

Hakan na zuwa ne bayan da wani kwamitin da Gwamna Ahmadu Umaru Fintiri ya kafa ya gudanar da bincike, wanda a cikin rahotonsa ya gano kura-kurai a daukar da aka yi wa ma`aikatan.

To sai dai ma’aikatan da aka dakatar sun musanta batun rashin cika ka’ida wajen daukar tasu.

Wata malamar kwalejin da sallamar ta shafa ta ce rayuwarta ta gigita tun bayan dakatarwar.

“Na karbi takardar nan, ina fita ban san inda kaina yake ba kawai sai na fadi. Duniyar gaba daya ta fita daga kaina ban san mene ne yake yi min dadi ba.

“Wata bakwai ina aiki ba a biya na. Kuma an tantance ni, ba ni da wata matsala. Iyayena ba su da karfi sannan ga marayu a gabana.”

Gwamnatin dai ta yi zargin cewa wasu ma`aikatan ba su da cikakkiyar shaidar kammala karatu ko kwarewa, yayin da wasu kuma take zargin gwamnatin da ta gada ce ta gaggauta daukarsu aiki a lokacin da wa`adinta ke gab da cika.

Sai dai wasu daga cikin ma`aikatan da aka sallama, sun ce babu gaskiya a hanzarin da gwamnatin ke kawowa.

Hasali ma dakatarwar ta shafi wasu ma`aikatan da ke wasu ma`aikatun gwamnati.

Sai dai gwamnatin jihar Adamawa a nata bangaren, ta ce har yanzu ba ta yanke shawara a kan makomar sauran ma`aikatan da ba na kwalejin fasahar ba, wadanda aka dakatar da su, kasancewar kawo yanzu ba a mika mata cikakken rahoto a kan su ba.

Gwamna Ahmadu Fintiri dai ya yi ikirarin kyautata rayuwar ma`aikata tun lokacin yakin neman zabe, abin da ke daure kai shi ne yadda gwamnatinsa ta fara sa kafar-wando guda da irin wadannan ma`aikata.

To sai dai da ma tun a lokacin da yake kaddamar da gwamnatinsa ya ce ba zai iya tafiya da ma`ikatan da gwamnatin da ya gada ta dauka aiki tana gab da shudewa ba.

More News

Magoya bayan APC da dama sun koma NNPP a Kano

Jam'iyar NNPP ta karɓi magoya bayan jam'iyar APC da dama a jihar Kano. Mataimakin gwamnan jihar Kano, Aminu Abdul Salam Gwarzo shi ne ya karɓi...

APC ta dakatar da Ganduje a matakin gunduma

Mambobin jam'iyyar APC a mazabar da ke Karamar Hukumar Dawakin Tofa a Jihar Kano sun dakatar da Shugaban Jam’iyyar APC na kasa Abdullahi Ganduje. ...

Yadda rikici a kan gishirin N20 ya yi sanadiyyar mutuwar wani mutum a Kano

Wani magidanci mai suna Zakari Hamza mai shekaru 45, ya gamu da ajalinsa a hannun kanen matarsa, wani Magaji Salisu saboda gishirin N20. Dan marigayin,...

Sojoji Sun Kashe Mayaƙan IPOB 5

Dakarun rundunar sojan Najeriya da kuma ta rundunar sojan ruwan Najeriya a ranar Talata sun kashe mayaƙan ƙungiyar IPOB guda biyar a yayin musayar...