An ci Arsenal karo na uku a jere a Firimiya | BBC Hausa

Unai Emery

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Arsenal ta kara barar da damar shiga cikin ‘yan hudun farko a gasar Premier, bayan da Leicester City ta doke ta 3-0 a karawar mako na 36 ranar Lahadi.

Jarmie Vardy ne ya ci wa Leicester City kwallo biyu, sannan Youri Tielemans ya ci daya a fafatawar da suka yi a King Power.

Arsenal ta kare wasan da ‘yan kwallo 10 a cikin fili, bayan da aka bai wa Ainsley Maitland-Niles jan kari a karawar.

Karo na uku kenan ana cin Gunners, bayan rashin nasara da ta yi a hannun Crystal Palace a Emirates da doke ta da Wolverhampton ta yi a Molineux.

Arsenal na nan a matakinta na biyar da tazarar maki daya tsakaninta da Chelsea ta hudu wadda za ta kece raini da Manchester United a yammacin Lahadin.

Ita kuwa Leicester City tana ta takwas da tazarar maki biyar tsakaninta da Wolverhampton ta bakwai, kuma su biyu na fatan shiga gasar Europa League ta badi.

Sai dai hakan ya danganta idan har Manchester City ta lashe kofin FA.

Wasannin da suka rage wa Arsenal:

Europa League 02 Mayu 2019

Premier League 05 Mayu 2019

Europa League 09 Mayu 2019

Premier League 12 Mayu 2019

More News

Yahaya Bello Ya Bayyana Dalilan Da Ya Hana Shi Bayyana A Gaban Kotu

Tsohon gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello ya ce tsoron kamun  hukumar EFCC dake yaÆ™i da yiwa tattalin arzikin Æ™asa ne ya hana shi bayyana...

Ƴan sanda sun kama mutane biyu dake samarwa ƴan fashin daji makamai a jihar Kaduna

Rundunar Æ´an sandan jihar Kaduna ta ce tana tsare da wasu mutane biyu da ake zargi da safarar bindiga a jihar. A wata sanarwa ranar...

An kori sojojin Najeriya biyu saboda satar kebul a matatar Dangote

Rundunar sojin Najeriya ta tabbatar da korar wasu sojoji biyu da ake zargi da satar igiyoyin sulke a harabar matatar Dangote da ke jihar...

Magoya bayan APC da dama sun koma NNPP a Kano

Jam'iyar NNPP ta karɓi magoya bayan jam'iyar APC da dama a jihar Kano. Mataimakin gwamnan jihar Kano, Aminu Abdul Salam Gwarzo shi ne ya karɓi...