Rundunar ƴan sandan birnin tarayya Abuja ta ce mutane uku aka ceto daga cikin baraguzan ginin bene da ya ruguzo a yankin Garki dake birnin tarayya Abuja.
Ƴan sanda sun bayyana sunan ginin da ya ruguzo da Unity House dake kan titin Nkwere kuma ya ruguzo ne ranar Litinin da daddare.
A wata sanarwa da aka fitar ranar Talata, Josephine Adeh mai magana da yawun ƴan sandan birnin ta ce, Benneth Igweh kwamishinan ƴan sandan birnin ya jagoranci tawagar jami’an ƴan sanda ya zuwa biyo bayan kiran kai ɗaukin gaggawa da rundunar ta samu.
Mai magana da yawun rundunar ta ce hukumomin da abun ya shafa na cigaba da saka idanu akan lamarin.