An ceto mutane 9 daga wani ginin bene da ya ruguzo a jihar Niger

Mutane 9 aka samu nasarar cetowa daga wani ginin bene mai hawa É—aya da ya ruguzo a yankin Sabon Gwari dake garin Minna babban birnin jihar Niger.

Da yake tabbatar da faruwar lamarin, Wasiu Abiodun mai magana da yawun rundunar Æ´an sandan jihar Niger ya ce ana amfani da ginin ne a matsayin rumbun ajiye kayayyaki.

Ya ce ginin ya ruguzo ne da misalin Æ™arfe 2:30 na ranar Juma’a.

Rahotanni sun bayyana cewa wasu mutane da ba a san yawansu ba ne ake tunanin baraguzan ginin ya binne su.

Abiodun ya ce biyu daga cikin mutanen da aka ceto sun samu karamin rauni.

An kai waÉ—anda aka ceto ya zuwa Babban Asibitin Minna domin samun kulawar likita.

More News

Muna aiki tukuru don kawar da aikata manyan laifuka a Najeriya—Tinubu ga Daraktan FBI

A ranar Juma’a ne shugaba Bola Tinubu ya karbi bakuncin daraktan hukumar binciken manyan laifuka ta kasar Amurka (FBI), Christopher Asher Wray, inda ya...

Sojojin sun kama wani mai safarar bindigogi a jihar Filato

Dakarun rundunar Operation Safe Haven dake aikin  samar da  tsaro a jihar Filato sun ka ma wani mai safarar  bindiga da ake nema ruwa...

Ƴan bindiga sun yi garkuwa da matafiya akan hanyar Abuja-Kaduna

Fasinjoji da dama ne aka bada rahoton an yi garkuwa da su bayan da ƴan fashin daji suka buɗe kan wata mota ƙirar bus...

Kotu ta yanke wa É—ansanda hukuncin kisa saboda laifin kisan kai

Wata babbar kotun jihar Delta dake zamanta a Asaba a ranar Talata ta yanke wa Sufeta Ubi Ebri na rundunar ‘yan sandan Najeriya hukuncin...