An bayar da belin yan shi’a sama da 100 da aka gurfanar a gaban kotu

Ƴansanda sun gurfanar da yan shi’a sama da mutane 100 a gaban wata kotun majistire dake Abuja inda ake zarginsu da ta da hankalin al’umma.

Cikin yan kungiyar ta shi’a sama da 100 da aka gurfanar a gaban kotun a ranar Alhamis, 10 daga cikinsu mata ne.

An kama sune ranar Talata lokacin wata zanga-zanga da ta rikide zuwa tarzoma a yankin Wuse dake Abuja.Sun dade suna zanga-zangar neman a saki shugaban su, Ibrahim Elzakzaky wanda ke hannun jami’an tsaro.

Ƴansanda sun ce cikin abubuwan da aka gano a tare da su har akwai kawalaben bom na fetur.

Dukkannin mutanen sun ki amsa tuhumar da ake musu kana sun nemi a a basu beli.

Kotun majistiren ta bayar da belinsu kan kudi kama daga ₦50000 zuwa ₦200000 da kuma mutanen da za su tsaya musu.

An dage zaman shari’ar ya zuwa ranar 5 ga watan Disamba.

More News

ÆŠalibai a Jami’ar Jos na zanga-zanga saboda rashin wuta da ruwa

Wasu daliban jami’ar Jos da ke jihar Filato a ranar Alhamis sun gudanar da zanga-zangar nuna rashin amincewarsu da matsalar karancin ruwa da rashin...

MTN yana ƙoƙarin ƙara kuɗin kati da data a Najeriya

Katafaren kamfanin sadarwa na MTN na kokarin kara kudin katin waya da na data a Najeriya. Kamfanin sadarwa mafi girma a nahiyar Afirka ya ba...

Gwamnatin Kano Ta Rage ₦500,000 A Kuɗin Aikin Hajjin Bana

Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf ya sanar da yiwa maniyatan Aikin Hajji da suka fito daga jihar kyautar ₦500,000 domin su cika kuɗin...

Ƴan bindiga sun sace wani limami a jihar Kogi

Ƴan bindiga sun yi garkuwa da Quasim Musa babban limamin garin Iyara dake ƙaramar hukumar Ijumu ta jihar Kogi. Lamarin ya faru ne a ranar...