An bankado euro miliyan 6 a gidan Omar al-Bashir

Omar al-Bashir

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Masu bincike sun gano euro miliyan 6 a gidan hambararren shugaban Sudan Omar al-Bashir.

Kwamitin yaki da cin hanci da rashawa da gwamnatin riko ta mulkin soja ta kafa a kasar ya bayyana cewa an gano kudade da dama a yayin wani samame da aka kai gidan tsohon shugaban.

Daya daga cikin ‘yan kwamitin ya shaidawa BBC cewa ayarin ‘yan sanda da kuma ‘yan sandan leken asiri sun bankado euro miliyan shida da kuma dalar Amurka 300,000 a gidan tsohon shugaban.

Ya kara bayyana cewa an gano kudin kasar Sudan da suka kai kimanin fam biliyan biyar inda ya ce an kai kudin banki domin ajiya.

Tuni dai aka tasa keyar tsohon shugaban kasar zuwa gidan yari na Kobar bayan tsare shi da aka yi a gidansa a lokacin da aka hambarar da shi daga kan karagar mulki.

Juyin mulkin da aka yi wa Omar ya biyo bayan wata doguwar zanga-zanga da ‘yan kasar suka fara tun a bara sakamakon tashin gwauron zabi na kayayyakin masarufi.

Da tafiya tayi tafiya zanga-zangar ta sauya akala inda masu zanga-zangar suka ci gaba da mamaye titunan babban birnin kasar na Khartoum da cewar lallai sai shugaban ya sauka.

A zanga-zangar da aka gudanar, an shaida cewa mata sun taka muhimmiyar rawa inda aka ce sune kashi biyu bisa uku na masu zanga-zangar.

Wane ne Omar al-Bashir?

Mista Bashir ya jagoranci mulkin Sudan tsawon shekara 30.

Ana zarginsa da shirya laifukan yaki da laifukan cin zarafin bil’adama a yankin Darfur na yammacin Sudan, wanda a dalilin haka ne kotun ICC ta aike masa sammaci.

Bayan watannin da aka shafe ana zanga-zanga – wadda aka fara sanadin tsadar rayuwa aka kuma yi ta kira ga shugaban don ya yi murabus kan hakan – sai a ranar Alhamis 11 ga watan Afrilu ne aka yi juyin mulkin da ya hambarar da shi.

An samar da kwamitin mika mulki na soji sakamakon hambarar da shi din, kuma an ce kwamitin zai ci gaba da aiki har tsawon shekara biyu zuwa lokacin da za a samar da gwamnatin farar hula.

Hukunci ga tsohon shugaban kasar?

Daga Will Ross, Editan BBC na Afirka

A lokacin mulkinsa na shekara 30, Omar al-Bashir ya daure da yawa daga abokan adawarsa na siyasa a gidan yarin Kobar. A yanzu ‘yan uwansa sun ce shi ma can aka kai shi.

Yanayin yadda gidan yarin yake abun kaduwa ne sosai idan aka kwatanta da daular da ke fadar shugaban kasa, inda a can aka yi masa daurin talala tun ranar Alhamis.

‘Yan Sudan da dama na fatan a hukunta tsohon shugaban nasu saboda ta’asar da aka tafka a lokacin mulkinsa.

Janar-janar din sojin da a yanzu ke tafiyar da kasar sun ce ba za a mika Mista Bashir ga kotun ICC ba, amma za a yi masa shari’a a Sudan.

Idan har suka ga ga hujja a bayyane cewa yana gidan yari, to masu zanga-zangar da ke neman a dawo da mulkin farar hula za su dan samu kwanciyar hankalin cewa lallai kasar za ta wuce zamanin mulkin kama karya.

More News

EFCC na neman Yahaya Bello ruwa a jallo

Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arzikin Kasa Ta’annati (Economic and Financial Crimes Commission) ta bayyana tsohon gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello a matsayin...

Mutane da dama sun mutu bayan motar fasinja ta taka bam a Borno

Akalla mutane 16 ne ake fargabar sun mutu yayin da wasu 20 suka jikkata bayan wata motar fasinja da ke kan titin Baga-Kukawa a...

Sojoji Sun Ceto Lydia Simon ĆŠaya Daga Cikin Ćłan Matan Chibok

Dakarun sojan Najeriya dake aiki da rundunar samar da tsaro ta Operation Desert Sanity III sun samu nasarar ceto, Lydia Simon É—aya daga cikin...

Gwamna da ƴansanda sun daƙile yunkurin EFCC na kama Yahaya Bello

A ranar Laraba ne Gwamnan Jihar Kogi, Usman Ododo, ya dakile wani yunkurin da Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arzikin Kasa Ta’annati ta...