An bai wa gwamnatin Buhari shawarar kara farashin fetur zuwa N302

Watakila gwamnatin Najeriya ta kara farashin man fetur zuwa naira 302 a kan kowa ce lita a wata mai zuwa, Fabrairu, kamar yadda majalisar kasa kan tattalin arziki ta bayar da shawara a watan Nuwamba na 2021

ta labarto.

Jaridar ta ruwaito cewa tana ganin wannan na daga cikin shirin gwamnati na janye hannunta kacokan daga harkar sanya farashin man, domin kawo karshen tallafin da take biya a kowane wata, ta yadda kasuwa za ta yi halinta a samu gogayya kan farashin.

A yanzu dai ana sayar da man fetur a yawancin sassan Najeriya a tsakanin naira 162 da 165 a kan kowace lita.

Kwamitin wucin-gadi na majalisar kula da tattalin arziki wanda ya tattauna da kamfanin mai na kasar (NNPC) a kan farashin da ya dace a sa shi ne ya bayar da shawarar kara kudin ta hanyar janye tallafin.

Gwamnan jihar Kaduna Mallam Nasir El-Rufai, wanda shi ne shugaban kwamitin, shi ya gabatar da rahoton.

More News

Kwankwaso ya ziyarci Obasanjo

Tsohon gwamnan Kano, Rabiu Musa Kwankwaso ya ziyarci tsohon shugaban kasa, Olusegun Obasanjo. Ziyarar ta Kwankwaso wani bangare ne na cigaba da tattaunawar...

Kwankwaso ya ziyarci Obasanjo

Tsohon gwamnan Kano, Rabiu Musa Kwankwaso ya ziyarci tsohon shugaban kasa, Olusegun Obasanjo. Ziyarar ta Kwankwaso wani bangare ne na cigaba da tattaunawar...

Sojojin sun kama tarin makamai a a hannun mayakan IPOB

Rundunar sojan Najeriya ta samu nasarar kama makamai da suka hada bindigogi hodar hada bam a jihar. Rundunar ta samu gagarumin wannan nasara ne biyo...

Atiku ya ziyarci mahaifiyar su Yar’adua

Mai neman takarar shugaban kasa a jam'iyar PDP, tsoshon mataimakin shugaban kasa, Alhaji Atiku Abubakar ya ziyarci mahaifiyar tsohon shugaban kasa, Umar Musa Yar'adua...