Connect with us

Hausa

Amurka ta tura karin dubban sojoji saboda barazanar Iran

Published

on

US Marine

Hakkin mallakar hoto
AFP

Ma’aikatar tsaro ta Pentagon ta sanar da tura karin dubban sojojin Amurka domin “Kara karfin kariya ga Saudiyya”.

Sakataren Tsaro na Amurkar, Mark Esper ya ce ya amince da aikewa da karin dakaru da suka hada da jiragen yaki da kuma na’u’rorin kariya.

Ya ce hakan martani ne ga “irin barazanar da yankin ke fuskanta”, a dai-dai lokacin da ake rubanya kokarin kare masarautar daga “hare-haren Iran”.

Wannan dai na zuwa ne bayan da aka kai har kan matatun man kasar Saudiyya a watan Satumba.

Yanzu haka dai Amurka ta kara dakaru 14,000 a yankin gabas ta tsakiya tun watan Mayu, kamar yadda gidan talbijin na CNN ya rawaito.

Tun dai lokacin da aka kai wa matatun man Saudiyya harin jirgi maras matuki, al’amarin da ya lalata su, ake ta zargin kasar Iran da hannu.

Tuni dai Iran ta musanta kai harin.

Su ma shugabannin kasashen France da Jamus da Burtaniya sun ce babu wata kwakkwarar sheda cewa Iran din ce ta kai harin.

Facebook Comments

Hausa

Yadda bindigar shaida ta harbe lauya a kotu | BBC Hausa

Published

on

Bindigar da aka kai kotu shaida
Image caption

An kai bindigar otu makare da harsashi a ciki

‘Yan sanda a Afirka ta Kudu sun ce wata lauya ta gamu da ajalinta, a lokacin da harsashi ya kufce bisa kuskure daga bindigar da aka kawo kotu dan kafa shaida da ita a yankin KwaZulu Natal.

Lauyar mai suna Adelaide Ferreira-Watt ta gamu da ajalinta jim kadan bayan harbin da bindigar ta yi ma ta a kwankwasonta.

Kunamar bindigar ta dana kanta a dai-dai lokacin da aka gabatar da ita a matsayin shaida gaban alkali kan fashi da makami da aka yi a wani gida,

‘Yan sanda sun ce su na gudanar da bincike kan mutuwar Miss Ferreira-Watt a matsayin kisa ba da gangan ba.

Za kuma su yi bincike kan dalilin da ya sa aka kawo bindigar kotu alhalin akwai harsashi a cikinta, dan hakan ya sabawa ka’ida.

Facebook Comments
Continue Reading

Hausa

Yadda aka cinna wa ‘yar jam’iyyar PDP wuta a kogi

Published

on

Kogi

Rahotanni sun nuna cewa wasu da ake zargin ‘yan dabar siyasa ne sun cinna wa wata shahararriyar ‘yar siyasa a Kogi wuta ranar Litinin.

Wasu jaridun Najeriya sun ruwaito cewa kakakin rundunar ‘yan sanda na jihar Kogi, William Aya ya bayyana cewa, Salome Abuh mai shekaru 60 wadda ita ce shugabar mata ta jam’iyyar PDP a mazabar Ochadamu a karamar hukumar Ofu, na barci a gidanta lokacin da ‘yan dabar suka cinna wa gidan wuta daf da magariba.

A wata sanarwa da mai magana da yawun rundunar, William Aya ya fitar, ta ce al’amarin ya faru ne ranar Litinin da misalin karfe 4:30 na yamma.

Sanarwar ta ce wani mai suna Musa Efu daga garin Ochadamu a karamar hukumar Ofu ya kai korafi a ofishin ‘yan sanda cewa an samu rashin jituwa tsakanin wani dan jam’iyyar PDP da wani dan jam’iyyar APC inda dan jam’iyyar ta PDP ya daba wa dan APC wuka a cinya.

Mutumin da aka caka wa wukar dai ya mutu a kan hanyar zuwa asibiti.

Hakan ne ya harzuka matasan yankin suka dunguma zuwa gidan kawun mutumin da ya yi kisan inda suka kona gidan abin da ya yi sanadiyyar kone da kashe Salome Abuh mai shekara 60.

Matasan sun kuma kone wasu karin gidaje uku.

Rundunar ‘yan sanda ta ce tana ci gaba da bincike domin gano mutanen da ake zargi.

Facebook Comments
Continue Reading

Hausa

Mikel Obi: Hazard Malalacin dan wasa ne

Published

on

Obi tare da Hazard lokacin atisaye

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Tsohon dan wasan Najeriya John Obi Mikel ya bayyana Eden Hazard a matsayin malalacin dan wasan da bai taba gani ba a kwallon kafa.

Obi Mikel dai sunyi wasa tare da Hazard a kungiyar kwallon kafa ta Chelsea a baya.

Kwarewar da Hazard din ya haifar shine ya sa ya sami damar komawa Real Madrid a bana, amma yadda yake taka leda a Bernabeu ya janyo ce-ce-ku-ce game da ingancin lafiyarsa.

Sai dai ana ganin dan wasan dan asalin Belgium zai iya nuna bajinta idan aka kwatanta yadda yake taka leda a Chelsea din a baya.

Mikel ya ce ‘Hazard yana da baiwa ta ban mamaki,’ musamman yadda yake sarrafa kwallo.

Watakila ba shi da kwarewa kamar [Lionel] Messi, amma yana iya yin duk abin da ya ga dama ya murza kwallo.

“Ba ya son karbar horo mai tsanani. Yayin da muke karba horo abinda ya yi face akai shi nei tsayuwa yana kallon mu.

“Amma a ranar lahadi ya bada mamaki kwarai, domin rawar da ya taka abin a yaba masa ne, ni kaina ya bani mamaki.”

Facebook Comments
Continue Reading

Trending

© Copyright 2019 - AREWANG Media Limited