Amurka ta bawa Najeriya tallafin allurar rigakafin cutar Mpox

Gwamnatin ƙasar Amurka ta bayar da gudunmawar allurar rigakafin cutar ƙyandar biri wato Mpox  a turance guda 10,000 domin taimakawa ƙoƙarin da Najeriya take shawo kan annobar cutar da ta ɓarke.

An bayar da tallafin ne ta hannu hukumar USAID ta  ƙasar Amurika dake tallafawa cigaban ƙasashe a yayin da Hukumar Bunƙasa Lafiya a Matakin Farko (NPHCDA) ta karɓi tallafin a madadin gwamnatin tarayya.

Da yake magana lokacin da yake miƙa tallafin a Abuja Richard Mills jakadan hukumar ta USAID a Najeriya ya shawarci gwamnatin tarayya da ta samar da kuɗaɗe domin sayo ƙarin allurar rigakafin domin shawo cutar ta Mpox.

Gwamnatin ta ce za ta mai da fifiko wajen bayar da rigakafin ga jihohin Bayelsa, Cross Rivers, Edo, Lagos da Rivers inda aka fi samun waɗanda suka kamu da cutar.

More from this stream

Recomended