Amurka da Burtaniya na zargin Taliban da laifukan yaki

Taliban ta kama yankuna da dama a Afghanistan a wata biyu da ya wuce fiye da yadda ta yi a baya tun bayan kifar da gwamnatinta a 2001

Asalin hoton, EPA

Bayanan hoto,
Taliban ta kama yankuna da dama a Afghanistan a wata biyu da ya wuce fiye da yadda ta yi a baya tun bayan kifar da gwamnatinta a 2001

Amurka da Burtaniya sun ce mai yuwuwa kungiyar Taliban da ke yaki a Afghanistan ta aikata laifukan yaki a hare-haren da take kaiwa a kwanan nan.

A sanarwar da suka sanya a shafin tuwita, ofisoshin jakadancin kasashen biyu da ke Kabul, sun yi bayani sosai a kan abin da suka kira kisan kiyashin farar hula a garin Spin Boldak da ke kan iyaka da Pakistan. Sai dai kungiyar Taliban ta yi watsi da zargin.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,
Gwamnatocin Amurka da Burtaniya na neman a yi bincike kan hare-haren Taliban da nufin gano laifin yaki

Kamar yadda wannan yaki yake kara tsananta a fadin Afghanistan, haka ma kuma ake kara nuna damuwa a kan irin keta haddi da cin zarafin da ake yi a fagen dagar.

Yawanci ana mayar da hankali ne a kan zargin keta haddi da saba ka’ida da mayakan Taliban ke yi ne, da suka hada da yadda suke kai wa sojojin gwamnatin Afghanistan da kuma farar hula hare hare.

A kwanan nan aka ga wasu hotunan bidiyo na irin keta haddi da tsabagen rashin Imani ko tausayi da mutunta dan adam, da aka yi a garin kan iyaka na Spin Boldak, abin da ya harzuka jama’a da hukumomi, wanda ya sa a yanzu Amurka da Burtaniya ke neman da a gudanar da bincike na yuwuwar gano laifukan yaki da aka aikata.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,
Sojojin Afghanistan na kokarin kwato wasu yankunan da suka fada hannun Taliban

A wadannan makonni na karshen ayyukan sojojin hadaka da Amurka ke jagoranta, gwamnatin Amurka na ta gargadin ‘yan Taliban, inda a fili take sukar hare-haren da suke kaiwa yanzu.

To amma kuma a Litinin din nan Shugaba Ashraf Ghani na Afghanistan, yayin jawabinsa a majalisar dokokin kasar, na cike da Amurkar, inda ya dora alhakin kazantar yakin da ake yi yanzu a kan matakin da gwamnatin Shugaba Biden ta dauka na janye dakarunsu.

Shugaban na Afghanistan ya ce, abin da ya jefa su halin da suke ciki yanzu shi ne saboda wata shawara da aka yanke.

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto,
Shugaba Ashraf Ghani ya ce matakin da Shugaban Amurka ya dauka na janye dakarun kasarsa ne ya jefa Afghanistan a halin da take ciki a yanzu

Ya fayyace cewa na gaya wa Shugaban Amurka, ina mutunta matakin naka, saboda, ra’ayinka ne, to amma na kwana da sanin yana da illa.

Kalaman Shugaban na Afghanistan sun zo ne yayin da ake ta suka a majalisar dokokin kasar ta Afghanistan, da kuma damuwa da bacin rai da jami’an Amurka da Burtaniya ke nunawa a bayan fage, cewa shirin Shugaba Ghani na soji ya gaza.

Ana ganin sakamakonsa a fili karara inda ‘yan Taliban ke ci gaba da mamaya a fadin kasar ta Afghanistan. Lamarin ya kai har ta kusa kama birni na biyu mafi girma a kasar, Kandahar.

Kuma rayuwar jama’a na cikin halin kaka-ni-kayi, kamar yadda shugaban wata kungiyar bayar da taimakon ilimi, Pashtana Durrani ya gaya wa BBC:

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,
Iyalai da dama sun rasa ta yi

Ya ce: ”Na yi kuka sosai da idona, saboda ba abin da ake yi sai harbe-harbe da ruwan bama-bamai duk tsawon dare, da kuma safiya. Ba abin da kake gani sai harsasai a bayan gidanka da gaban gidanka.

Duk lokacin da ka duba wayarka za ka ga wani a cikin ‘yan uwanka ya mutu, wani a gundumarku ya mutu, wani da ka sani ya mutu, wani da ka sani na gudu daga kasar, wani da ka sani na tserewa daga lardin, wannan kawai kana rayuwa ne cikin tashin hankali.”

More News

EFCC na neman Yahaya Bello ruwa a jallo

Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arzikin Kasa Ta’annati (Economic and Financial Crimes Commission) ta bayyana tsohon gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello a matsayin...

Mutane da dama sun mutu bayan motar fasinja ta taka bam a Borno

Akalla mutane 16 ne ake fargabar sun mutu yayin da wasu 20 suka jikkata bayan wata motar fasinja da ke kan titin Baga-Kukawa a...

Sojoji Sun Ceto Lydia Simon ĆŠaya Daga Cikin Ćłan Matan Chibok

Dakarun sojan Najeriya dake aiki da rundunar samar da tsaro ta Operation Desert Sanity III sun samu nasarar ceto, Lydia Simon É—aya daga cikin...

Gwamna da ƴansanda sun daƙile yunkurin EFCC na kama Yahaya Bello

A ranar Laraba ne Gwamnan Jihar Kogi, Usman Ododo, ya dakile wani yunkurin da Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arzikin Kasa Ta’annati ta...