Amuneke ya karbi jan aikin horas da El-Makkasa

Amuneke

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Tsohon dan wasan Najeriya, Emmaneul Amuneke ya ce zai fuskanci babban kalubale, bayan da ya karbi aikin horas da El-Makkasa.

El-Makkasa mai buga gasar Premier ta Masar tana cikin ‘yan kasa-kasan teburi, inda Amuneke zai ja ragama zuwa karshen kakar bana.

Amuneke, mai shekara 49, zai maye gurbin Ahmed Hossam Mido ranar Asabar, kuma zai zama mai horas wa na hudu da kungiyar ta dauka a shekara uku.

Wannan karon Amuneke zai koma Arewacin nahiyar Afirka da sana’ar horas da tamaula, bayan da a baya can ya taka leda a yankin.

Tsohon dan kwallon Barcelona da Sporting Lisborn, ya koma Zamalek daga Julius Berger ta Lagos a 1991.

Amuneke ya ja ragamar tawagar Tanzaniya a karon farko tun bayan 1980 da kasar ta kai gasar cin kofin nahiyar Afirka.

Sai dai kasar ba ta taka rawar gani ba, inda aka yi waje da ita a wasannin cikin rukuni, hakan ne ya sa Amuneke da hukumar kwallon kafar Tanzaniya suka raba gari cikin fahimtar juna.

Amuneke ya horar da matasan tawagar kwallon kafa ta Najeriya da kuma kungiyar Sudan mai suna SC Khartoum.

More News

An kori sojojin Najeriya biyu saboda satar kebul a matatar Dangote

Rundunar sojin Najeriya ta tabbatar da korar wasu sojoji biyu da ake zargi da satar igiyoyin sulke a harabar matatar Dangote da ke jihar...

Magoya bayan APC da dama sun koma NNPP a Kano

Jam'iyar NNPP ta karɓi magoya bayan jam'iyar APC da dama a jihar Kano. Mataimakin gwamnan jihar Kano, Aminu Abdul Salam Gwarzo shi ne ya karɓi...

Sojoji sun gano masana’antar Æ™era bom a jihar Borno

Dakarun rundunar sojan Najeriya sun gano wata masana'anta da mayaƙan kungiyar ISWAP suke ƙera bama-bamai. Masana'antar ƙera bama-bamai an gano ta ne a Abulam-BUK dake...

Atiku ya ziyarci Abdul Ningi

Tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar ya ziyarci dakataccen ɗan majalisar dattawa sanata, Abdul Ningi dake wakiltar mazaɓar Bauchi ta tsakiya a majalisar dattawa. Atiku...