Amsar tambayoyinku kan nau’ukan haraji a Najeriya

  • Nabeela Mukhtar Uba
  • Broadcast Journalist

Wannan maƙala ce ta musamman bayan da muka buƙaci mabiyanmu da masu saurare su aiko da tambayoyinsu kan abin da suke son sani game da tsarin biyan haraji a Najeriya.

BBC Hausa ta duba tambayoyin naku kuma ta miƙa su ga masana da masu ruwa da tsaki a fannin na haraji.

Mene ne haraji?

Tambaya ce da muka samu daga Maruma Ibirahim da wasu da dama da ba su rubuta sunayensu ba

Dakta Shamsuddeen Muhammad, masanin tattalin arziki a Jami’ar Bayero ta Kano da ke Najeriya, ya bayyana haraji a matsayin wani kuÉ—i da gwamnati ta wajabta wa jama’a biya.

“Wani kuÉ—i ne na dolen-dole da gwamnati take É—ora wa Æ´an Æ™asa ko dai a kan kuÉ—in da suke samu a wurin sana’o’insu ko kuma a kan riba da suke samu a kasuwancinsu,” in ji shi.

Masanin ya ƙara da cewa kuɗaɗen harajin da gwamnati take karɓa suna taimaka wa gwamnatin wajen samun kuɗaɗen shiga.

Amfanin haraji

Tambaya ce da muka samu daga Mukhtar Muhammad Ngibirma da Abdulrasheed Kaku Unguwan Sarki Kaku da Nazifi Lawal Batsari da Siraja Abubakar da Ibrahim mai Indomie da Abbakar Usman

Masanin tattalin arzikin ya ce zai yi wuya a iya rarrabe amfanin haraji ga mutane da kuma gwamnati saboda “kamar gwamnatin ita ce mutane.”

Amma ya bayyana wasu kamar haka:

Samar da ayyukan more rayuwa

Bayanan hoto,
Daga cikin ayyukan da ake da kuÉ—aÉ—en haraji har da gina abubuwan more rayuwa

Masanin ya bayyana cewa ana karÉ“ar haraji ne domin bai wa gwamnati damar gudanar da ayyukan more rayuwa ga al’ummarta kamar ruwan sha da wutar lantarki da tituna da tallafi da gwamnati ke bayarwa lokacin da aka shiga wasu matsaloli.

Rage amfani da abubuwa masu cutarwa

Baya ga samar da ayyukan ci gaba a Æ™asa, masanin ya Æ™ara da cewa harajin yana da amfani saboda yana rage amfani da abubuwa masu cutarwa inda ya ba da misali da kamfanonin giya da taba a Najeriya, wadanda suke biyan haraji mai nauyi wanda ya kai kusan kashi 20 cikin É—ari na kayan da suke samarwa “saÉ“anin kashi bakwai da rabi na sauran kayan masarufi.”

Ya ce ana yin haka ne domin rage yawan shan barasa da kuma taba sigari a Æ™asar, “shi haraji idan an sa wa kaya sun yi tsada sosai, lalle mutane za su rage shansu maimakon wataÆ™ila mutum ya sha kara 10 na sigari a rana, sai ya sha kara biyu ko uku ko biyar.”

Gyara muhalli

Ana amfani da haraji wajen gyara muhalli – “duk inda masana’antu suke suna taimaka wa wajen lalacewar muhalli, ta lalata ruwan sha da iska da sauransu.

”Idan ana É—ora haraji mai nauyi kan irin waÉ—annan dagwalon masana’antu ke zubarwa su masana’antun suna Æ™oÆ™arin rage abin da suke zubarwa na dagwalon wanda wannan yana taimakawa haraji Æ™warai da gaske,” in ji Dakta Shamduddeen Muhammad.

Taƙaita shigo da kaya daga ƙasashen waje

A cewar masanin, wani ƙarin amfanin harajin shi ne yana rage shigo da kaya daga ƙasashen waje domin bunƙasa kamfanonin cikin gida.

“Misali, kayan da gwamnati ba ta so a shigo da su waÉ—anda take ganin za a iya yinsu a cikin gida sai ta É—ora musu haraji mai yawan gaske, waÉ—anda idan an kawo su a cikin gida ba za su sayu ba sai dai misali sani na cikin gida,” a cewar masanin.

Gyara tattalin arziki

Ana amfani da haraji wajen cimma wannan buÆ™ata “duk lokacin da hauhawar farashi ta yi yawa cikin Æ™asa mafi yawa abin da yake faruwa kuÉ—i ne yake yawa a hannun jama’a sai gwamnati ta É—ora haraji a kan mutane ta rage yawan kuÉ—in da yake hannun mutane (ta yadda) mutane ba za su iya sayan abubuwan da suke so ba, wannan zai rage yawan buÆ™atar abubuwa a kasuwa.”

Ya ce a duk lokacin da aka samu buƙatar abubuwan da mutane suke so a kasuwa hakan yana sa farashi ya sauka.

A cewar masanin karɓar haraji na taimakawa wajen samar da ayyukan yi inda ya ba da misali da yadda a wani lokacin matsalar rashin aikin yi take yawa.

“A wannan lokacin abin da gwamnati take yi shi ne rage yawan haraji a kan mutane domin su samu kuÉ—aÉ—e da yawa a hannunsu da za su kashe a kasuwanni, idan sun kashe kuÉ—i da yawa a kasuwanni, masana’antu za su samu damar yin kayayyaki da yawa saboda akwai ciniki a kasuwa, wannan zai taimaka su É—ebi ma’aikata da yawa,” kamar yadda masanin ya shaida wa BBC.

Rage bambancin arziki tsakanin ƴan ƙasa

Ana kuma amfani da haraji wajen daidaita tsakanin ƴan ƙasa ta fuskar tattalin arziki saboda masu wadata sun fi biyan haraji mai yawa yayin da waɗanda talakawa suke biyan haraji ɗan kaɗan ko ma ba sa biya.

Ƙarin maƙaloli masu alaƙa

Masanin ya ce haraji ya rabu gida biyu – na kai tsaye da wanda ba na kai tsaye ba.

Harajin kai tsaye

Wannan haraji a Turancin Ingilishi ana kiransa Direct Tax. Wannan haraji ne da ya shafi mutum kai tsaye da zai biya daga albashinsa ko kuma idan kamfani ne zai biya daga ribarsa.

Ana kiransa haka ne saboda shi ya shafi mutum kai tsaye.

Ya ce akwai ire-iren haraji da suka faÉ—o a Æ™arÆ™ashin wannan nau’i na haraji kamar harajin da mutum zai biya kai tsaye daga albashinsa wato Personal Income Tax ko Pay As You Earn da kuma harajin da ake cira daga ribar kamfanoni wato Profit Tax.

A cewarsa, duk ribar da kamfani ya samu a shekara zai ware wani abu ya bai wa gwamnati wani abu cikin ribar.

Harajin da ba na kai tsaye ba

Tsarin wannan harajin shi ne mutum ba a cikin kuÉ—insa zai biya ba. “Misali harajin kayayyaki da ake sana’antawa, idan mai kamfani ya biya harajin kayan da ya sana’anta zai Æ™ara waÉ—annan kuÉ—aÉ—en a kan kayan da ya sana’anta domin sayarwa,” in ji Dakta Shamsuddeen Muhammad.

Sai dai masanin ya ce a Æ™arshe nauyin harajin yana Æ™arewa ne a kan mai saye “wanda ya biya daban wanda kuma nauyin harajin ya faÉ—a a kansa daban.”

A Æ™arÆ™ashin wannan nau’i na haraji akwai wanda ake biyawa kayan masarufi wato VAT – “shi kamfanin da yake ba wa gwamnati harajin ba shi ne yake bai wa gwamnati haraji ba, kwastomomi waÉ—anda suke sayen kayan su ne suke biyan harajin.”

Akwai kuma harajin kuÉ—in fito wato Customs Duty ko Import da Export Duty- “idan mutum ya shigo da kaya na sayarwa daga Æ™asar waje, zai biya musu haraji amma zai Æ™ara wannan haraji kan farashin kayan inda shi wanda zai kayan ya yi amfani da su shi ne wanda harajin zai Æ™are a kansa,” in ji masani Dakta Shamsuddeen Muhammad.

Wannan haraji na kuɗin fito yana haura harajin VAT a Najeriya amma akwai ƙasashe na duniya musamman waɗanda suka ci gaba wanda shi harajin na VAT shi ne mafi yawan harajin da gwamnati take karɓa a kowanne lokaci.

Ya ce akwai wasu kuÉ—aÉ—en shiga da ake biya kamar tara ko kuma Levy wanda ake É—orawa a kan amfani da kayan gwmanati kamar masu haÆ™ar ma’adinai da Æ™arafuna da gwal suna biyan kuÉ—in hayar Æ™asa wato Royalties ko kuma Lease.

Sai kuma tara ta kotu da ake biya ko kuma idan mutum ya yi laifi a É—ora masa wata tara – “ba haraji ba ne na kai tsaye amma yana cikin kuÉ—aÉ—en shiga da gwamnati take samu,” a cewar masanin.

Harajin kayan masarufi wato VAT

Tambaya ce da muka samu daga Abbas Jobi da Abdulazeez Abubakar Baba da Nura Muhd Sani da Jamilu Bala Abdulkadir da Ibrahim mai indomie da Hussaini Mukhtar Isah Fagge da Abubakar Jidda da Farouk Ado Danmaliki da Yahaya Musa da Mustapha Magaji Muhammad

Shi wannan haraji ana biyawa kayan masarufi ne kuma kamfanonin cikin gida ne suke ɗora wannan haraji a kan kuɗin kayansu amma wannan ƙarin da suka yi na haraji ba nasu bane na gwamnati ne.

Dakta Shamsuddeen ya ce: “Idan mutane sun sayi kayan za su cire wannan kaso na haraji sai su bai wa hukumar da take karÉ“ar haraji na gwamnatin tarayya.”

Ya ce irin wannan harajin yana daga cikin manya-manyan haraji da gwamnati take karÉ“a kuma ana É—ora shi a kan dukkan kayan masarufi da ake sana’antawa a cikin Æ™asa ban da waÉ—anda gwamnati ta ga dama tace ban da su saboda wasu dalilai.

“Kamar misali mu a nan Najeriya, an ce duk abin da ya shafi kayan abinci da kayan ilimi da kayan lafiya – waÉ—an nan su ba za a É—ora musu harajin VAT ba amma bayan su duka sauran abubuwan da sauran Æ´an Æ™asa suke amfani da su har wutar lantarki duka wannan haraji na VAT yana kansu,

Yadda yake shi gwamnati tana ɗora wani kaso na kai tsaye da za ta ce komai za a sayar za a ƙara wannan kaso a kan kuɗinsa wanda shi wannan kason shi ne VAT ɗin wanda gwamnati ce za ta karɓe shi.

Misali a Najeriya yanzu, kason da ake biya na harajin VAT kashi bakwai da rabi cikin É—ari ne wanda ya Æ™aru daga kashi biyar da da ake biya a wannan shekarra a watan Fabrairu aka Æ™ara shi daga kashi biyar cikin É—ari zuwa kashi bakwai da rasbi cikin É—ari,” in ji masanin.

Wasu labaran da za ku so ku karanta

Harajin Stamp Duty

Tambaya ce da muka samu daga Salisu Dayyabu

Masana sun ce wannan haraji na Stamp Duty ɗaya daga cikin tsofaffin harajin da ake biya a duniya kuma ya samo asali ne daga Daular Sufaniya tun ƙarni na 17 kimanin kusan shekara 400 kenan.

Hatimi ne na gwamnati da ake bugawa a kan takardu waÉ—anda ake amfani da su wurin wata yarjejeniya ko kuma ciniki – takardu irinsu chekin kuÉ—i da takardar lasisin aure ko takardar sai da filaye duka suna buÆ™atar gwamnati ta buga hatiminta a kai domin ya zama cewar su waÉ—an nan takardu sun zama masu amfani kuma ko da kotu aka je waÉ—an nan takardu za su iya zama shaida saboda ga hatimi na gwamnati an buga a kai.

“Duk wanda ya yi irin wannan ciniki ko kuma suka yi irin wannan yarjejeniya ko kuma suka yi irin wannan yarjejeniya har gwamnati ta buga hatimi a kai sai a biya gwamnati kuÉ—i na hatimin da ta buga. Amma tun wannan lokaci gwamnatoci na duniya daban-daban suna amfani da wannan tsari har muka kawo zamanin da yanzu yawanci cinikayyar ba a yin ta fuska da fuska, yawanci cinikayya ce da ake yi ta kafofin sadarwa na zamani ko ta imel ko ta sauran kafafe na sadarwa na zamani,

Sai gwamnati a baya-bayan nan ta ga cewa tun da yanzu ba a amfani da takardu na zahiri, me zai hana shi wannan Stamp Duty da ake biyawa takardu na zahiri ya koma kan har irin waÉ—an nan kasuwanci da ake yi ta kafafen sadarwa na zamani.

Mu a nan a Najeriya daga watan Fabrairu, gwamnati ta Æ™irÆ™iro cewa duk musayar kuÉ—i da aka yi ta bankuna – wani ya tura wa wani kuÉ—i in dai sun kai N10,000 sai ya biya wa wannan kuÉ—i abin da ake cewa Stamp Duty É—in saboda a wajen gwamnati tana ganin duk wanda ya tura kuÉ—i har ya kai N10,000 ko sama da haka, lalle cinikayya aka yi,” in ji masanin.

Abin da gwamnatin Najeriya take samu daga harajin VAT

KuÉ—aden da gwamnati take samu daga harajin kayan masarufi suna hawa da sauka ne – ya danganta da yadda harkar tattalin arziki ta gudana a kowane wata tun da kuÉ—in ana karÉ“arsu ne wata-wata.

“A baya-baya lokacin da ake cikin wannan lalura ta Covid-19, kuÉ—in da ake karÉ“a na harajin VAT baya wuce N100bn amma a watan Agusta, kuÉ—aÉ—en da gwamnati ta karÉ“a ya kai sama da N150bn,

Dakta Shamsuddeen Muhammad ya ce: “Shi harajin VAT mafi yawa gwamnatocin jihohi da Æ™ananan hukumomi ne suka fi morarsa, duk da cewa gwamnatin tarayya ce take karÉ“a amma idan an zo rabon arzikin Æ™asa na wata-wata kusan kashi 86 cikin 100 na abin da aka karÉ“a na VAT yana tafiya ne ga gwamnatocin jihohi da Æ™ananan hukumomi.

A watan Agustan da ya gabata duk da dai an karÉ“i kuÉ—i har N150bn abin da gwamnatin tarayya ta mora a ciki bai wuce N20bn, ragowar kusan N130bn an raba su ne tsakanin Æ™ananan hukumomi da jihohi – jihohi sun rabauta da N70bn su kuma Æ™ananan hukumomi suka samu abin da bai fi N60bn.”

Ina kuÉ—in haraji ke tafiya da yadda ake sarrafa shi?

Tambaya ce da muka samu daga Ahmed Alim da Ahmad Tukur

Akwai wani asusu da ake kira Federation Account a Turancin Ingilishi wani asusu ne da ake buɗe shi a babban bankin ƙasa wanda ake zuɓa kuɗaɗen harajin a kowane wata.

Aannan a haɗa da sauran kuɗaɗe da gwamnati take samu ta hanyar sayar da mai a tara su sai sun taru a ƙarshen wata sai a raba su tsakanin gwamnatin tarayya da gwamnatocin jihohi da ƙananan hukumomi, wanda kwamitin FARC da aka ɗorawa alhakin rarraba arziƙin ƙasa yake yi a kowane wata.

Game da sarrafa kuɗaɗen harajin kuma, gwamnatocin a matakan uku suna amfani da kuɗaɗen wajen biyan bashi da yi wa ƙasa hidima da samar da abubuwan more rayuwa musamman manya-manyan ayyuka irinsu tituna da sauransu.

Su wane ne suke da ikon karɓar haraji?

Masanin tattalin arzikin ya bayyana cewa akwai harajin da gwamnatin tarayya da gwamnatin jiha da kuma ƙananan hukumomi suke karɓa.

A cewarsa: “Manya-manyan haraji na Æ™asa kamar wanda ake cirewa a albashi, kamar wanda ake biya na shigo da kayayyaki ko fito da su da na wanda manya-manyan kamfanoni suke biya a cikin Æ™asa, waÉ—an nan duka gwamnatin tarayya ce take karÉ“arsu.”

Bayanan hoto,
Hukumar FIRS ce ke da alhakin karɓar haraji a Najeriya

Baya ga waɗannan akwai kuma wasu harajin da gwamnatin jiha da ƙananan hukumomi suke karɓa kamar harajin kasuwanni da harajin tashoshi da harajin masu sufuri da sauran abubuwa da suka danganci ƙananan haraji.

Mafi yawan Æ™ananan hukumomi akwai sassa da suke kula da karÉ“ar haraji a kasuwanni ko a tashoshi ko a hannun masu sufuri sannan su ma gwamnatocin jihohi suna da ma’aikata guda da take karÉ“ar haraji domin gudanar da ayyuka ga Æ´an Æ™asa.

Ita ma gwamnatin tarayya tana da babbar hukumar da take tattara mata haraji – Hukumar FIRS sai hukumar kwastam wadda take da alhakin karÉ“ar harajin kayan fito na shige da ficen kayayyaki sannan ta miÆ™a su hannun hukumar karÉ“ar haraji ta Æ™asa.

Akwai kuma Æ™ananan ma’aikatu na gwamnati da suke karÉ“ar haraji da tara da ake É—orawa mutane kamar Hukumar Aika SaÆ™onni ta Najeriya (NIPOST) da kotuna da suke É—ora tara a kan wanda suka yi laifi da sauran hukumomi masu tsaron kan hanya.

Ita kanta kamfanin sarrafa albarkatun man fetur NNPC ita ma tana karÉ“ar haraji na haÆ™ar man fetur daga wajen waÉ—anda aka yarjewa su dinga haÆ™a sannan ma’aikatar kula da ma’adanai tana da alhakin karÉ“ar kuÉ—in hayar Æ™asa da take bai wa kamfanoni ko mutanen da suke haÆ™ar ma’adanai a cikin Æ™asa.

Duka waÉ—annan mafi yawa sun fi karÉ“ar tara ko kuma kuÉ—in haya yayin da hukumar FIRS da ta kwastam suke karÉ“ar haraji ka tsaye a madadin gwmanatin tarayya.” a cewar masanin.

Hanyoyin karɓar haraji

Tambaya ce da muka samu daga Idrisir abdullahi da Jabir garba kauran wali da Farouk Ado Danmaliki

A cewar masani Dakta Shamduddeen Muhammad, dangane da hanyoyin karÉ“ar haraji, ya danganta da irin harajin inda ya ba da misali da harajin da wanda ma’aikaci yake biya daga albashinsa, idan kuma ma’aikacin gwmanati ne dama gwamnati ce ke biyan albashi kuma za ta É—ebe harajin tun daga tushe sannan ta turawa hukumar da take biyan albashi, harajin kuma sai ta turawa hukumar da take karÉ“ar harajin.

Idan kuma kamfani ne, kowane kamfani a ƙarshen shekara zai rubuta ribar da ya samu a shekara sannan ya ware kason biyan haraji ya je ya shigar wa hukumar tattara haraji wannan kuɗi a banki, sannan ya kai shaidar cewa ga abin da ya ci riba ga kason haraji da ya biya su kuma su ba da takardar cewar ya biya haraji a wannan shekarar.

Idan ya Æ™i yin hakan akwai hanyoyi da ita hukumar karÉ“ar haraji ta Æ™asa take bi don tabbatar da ta karÉ“i wannan haraji – tun daga amfani da jami’an tsaro har zuwa kotuna har ma a Æ™arshe idan kamfani ya kasa biyan haraji a rufe kamfanin ko ma a sayar da shi kuma gwamnati ta É—ebi kuÉ—inta a cikin kadarorin kamfanin.

Shin gwamnati tana abin da ya dace da kuÉ—aÉ—en harajin?

Masanin tattalin arzikin ya ce ba za a ce gwamnati ba ta yin komai ba saboda “komai lalacewa a Æ™alla kusan kowane wata gwmanati za ta biya ma’aikata albashi sannan abubuwan da ba a rasa ba na gudanar da gwmanati na harkokin ilimi da harkokin lafiya duka gwmanati za ta yi ko da bai kai yadda mutane suke tsammani ba.

Sai dai ya ce matsalar ita ce “ana zargin cewa idan an ware wasu kuÉ—aÉ—en domin yin wasu ayyukan a cikin Æ™asa ana samun É“atagari a cikin waÉ—anda suke riÆ™e da madafun iko ko waÉ—anda aka É—orawa alhakin yin waÉ—annan ayyuka sai su É—ebe wani kaso na wannan kuÉ—aÉ—e da aka ware don yi wa jama’a aiki, sai su kwashe kuÉ—aÉ—en gaba É—aya su zuba a aljihinsu ko ma a (asusunsu) kuma su Æ™i yin wannan aiki ko kuma su yi shi rabi da rabi su yi shi ba yadda ya dace ba su kwashe ragowar kuÉ—aÉ—en.”

Inganta tsarin haraji da amfani da shi

A cewar Dakta Shamsuddeen Muhammad ya ce Najeriya tana É—aya daga cikin Æ™asashen da aka yi Æ™iyasin cewa kuÉ—aÉ—en harajin da ‘yan Æ™asa suke Æ™in biya ya yi yawa saboda a shekarar 2019, shugaban hukumar karÉ“ar haraji ya ce gwmanati tana kusan asarar naira triliyan biyar a harjin da ba a karÉ“a ba kuma laifin ya haÉ—a da mutanen da suke biyan haraji da kuma hukumomin da suke karÉ“ar harajin.

“Su mutane dama kowa zai yi Æ™oÆ™arin Æ™in biyan haraji har sai dai idan ya ga ba yadda zai yi gwmanati ta tilasta shi, idan ya ga cewa gwmanati ba ta san da shi ba ko kuma gwmanati ba za ta san nawa ya kamata ya biya ba, wannan abu ne na rashin nuna kishin Æ™asa da kuma daÆ™ile harkar ci gaba a cikin Æ™asa domin wannan haraji da mutane za su biya da shi ne gwmanati za ta yi wa mutane aiki.

Wani lokacin kuma matsalar tana faruwa ne daga hukumomin da suke karɓar harajin su ne suke haɗa baki da abokansu ko ƴan uwansu da suke da kamfanoni su nuna musu ba ma sai sun biya haraji ba su nuna musu kamar taimaka musu suke yi abin da ya kamata ka biya sai ka biya abin da bai kai rabinsa ba.

Kuma su hukumomin da suke karÉ“ar harajin ko kuma jami’ansu sun san cewa abin da ka biya ba shi yakamata ka biya ba abin da za ka biya ya ninka haka amma sai su yi shiru saboda wata alaÆ™a da take tsakaninsu ko kuma saboda za ka É—ebi wani abu na wannan kaso na abin da ba ka biya ba su ma ka ba su su zuba a aljihinsu.”

Amma ya ce yadda yake ganin za a gyara lamarin shi ne kowa ya sa tsoron Allah da kishin ƙasa da son ci gaban ƙasa a zuciyarsa wanda ya ce rashin haka babbar matsala ce.

Illar rashin biyan haraji

Shiga garari

Masanin ya ce babbar illar rashin biyan haraji shi ne gwamnatin Najeriya za ta koma dogaro ne da kuÉ—aÉ—en da take samu daga sayar da mai da sauran ma’adanai – “duk sanda kuÉ—in man fetur ya faÉ—i a kasuwar duniya, Æ™asar tana shiga garari tana shiga wani hali saboda mutane ba sa biyan harajin da ya kamata, kowa a Æ™asar sai ya shiga wahala, tsadar rayuwa ta yi yawa, talauci ya yi yawa rashin aikin yi ya yi yawa.

Yawan ciyo bashi

Wata matsalar ta haÉ—a da yawan basussukan da gwamnati take ciyowa domin ta samu ta yi ayyukan da suka zama wajibi ko kuma take son yinsu.

Ya ce da gwamnati tana samun isassun kuɗaɗen harajin wataƙila da ba sai ta dangana da ciyo bashin ba.

More News

Majalisar dokokin jihar Kaduna ta nemi ma’aikatar kudin jihar ta miÆ™ata bayanan bashin da El-Rufai ya ciwo

Majalisar dokokin jihar Kaduna ta nemi ma'aikatar kudi ta jihar da ta miƙa mata cikakken bayani kan basukan  da gwamnatin tsohon gwamnan jihar, Nasiru...

An dakatar da ayyukan kamfanin jiragen sama na Dana Air

Festus Keyamo, ministan harkokin sufurin jiragen sama ya umarci hukumar FAAN dake lura da sufurin jiragen sama a Najeriya ta dakatar da ayyukan kamfanin...

Yahaya Bello Ya Bayyana Dalilan Da Ya Hana Shi Bayyana A Gaban Kotu

Tsohon gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello ya ce tsoron kamun  hukumar EFCC dake yaÆ™i da yiwa tattalin arzikin Æ™asa ne ya hana shi bayyana...

Ƴan sanda sun kama mutane biyu dake samarwa ƴan fashin daji makamai a jihar Kaduna

Rundunar Æ´an sandan jihar Kaduna ta ce tana tsare da wasu mutane biyu da ake zargi da safarar bindiga a jihar. A wata sanarwa ranar...