Connect with us

Entertainment

Amokachi ya taya Mansurah da Sani Danja murnar shekara 12 da yin aure

Published

on

Mansurah da Sani Danja

Hakkin mallakar hoto
@mansurah_isah

Tsohon dan wasan Super Eagles na Najeriya Daniel Amokachi ya taya jaruman Kannywood Mansurah Isah da mijinta Sani Danja murnar cika shekara 12 da aurensu.

Sani Danja da Mansurah suna cikin ‘yan fim na farko-farko da suka auren juna, kuma sakon da suka wallafa a shafin Instagram ya ja hankalin jama’a sosai ciki har da tsohon dan kwallon na Najeriya.

A cikin sakon da tsohuwar jarumar fina-finan na Hausa ta wallafa mai dauke da hoton mijinta, ta yi takaitaccen bayani game da rayuwar aurensu na zaman hakuri da kaunar juna.

Kalaman sun nuna yadda kamar a gidaje da dama, ma’auratan ke zaman hakuri duk da irin sabanin da ta ce suna samu a lokaci zuwa lokaci.

Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da ake yawan samun rahotanni marasa dadin ji na yawaitar mutuwar aure a arewacin Najeriya da kuma kisa ko kaiwa juna hari tsakanin wasu ma’auratan, lamarin da ake alakantawa da rashin soyayya, hakuri da rashin bin tsari mai kyau wurin assasa auren.

Mansurah ta ce dukkaninsu suna da rauni, inda wani lokaci takan yi gaba da mijinta ba tare da ya saba mata ba, yayin da wani lokaci kuma ya ki cin abincinta har ya ki ba ta kudi idan ta tambaye shi.

“Ka ci gaba da hakuri da ni ka ci gaba da dauke kai a kan laififfuka na. Domin nasan ni mai laifi ce a gare ka. Rayuwa ba ka taba zama 100% komin yaya akwai inda ka kasa,” in ji ta.

Amma ta ce sukan yi dariyar sabanin da suke samu saboda sun zama abokan juna. Kuma har yanzu suna son junansu kuma suna taimakon juna.

Hakkin mallakar hoto
Michelly Rall

Image caption

Daniel Amokachi ya shahara wurin taka kwallo a ciki da wajen Najeriya

Ta kuma yaba wa yadda ta ce mijin nata ya yi hakurin zama da kuma kula da ita.

Kalaman sun sa mutane da dama yi mata da mijinta fatan alheri da dorewar zaman lafiya a aurensu, kuma cikinsu har da Daniel Amokachi.

Amokachi ya yi masu addu’a inda ya ce Allah Ya ci gaba da ba su zaman lafiya da kara kauna, bayan ya taya su murna.

Hakkin mallakar hoto
Awwal Ahmad

Wata daga cikin wadanda suka yi tsokaci ta ce, kalaman Mansurah sun kusan sa ta yin kwalla. Inda ta yi addu’a cewa Allah Ya kara daidaita tsakaninsu.

Mabiya sama da 800 ne suka yi tsokaci, yayin da kusan mabiya 15,000 suka so sakon.

Facebook Comments
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Entertainment

BBNaija: What I’ll do to any male housemate who makes move at Mercy – Ike

Published

on

Big Brother Naija, BBNaija housemate, Ike has threatened to deal with any male housemate that tries to get close to Mercy.

DAILY POST recalls that Ike again on Saturday night professed his love for Mercy.

But, Mercy, also reassuring him of her love maintained that although she loves him, he needs to know that his parents love him more than she does and he has to open up his mind to love them in return.

Ike speaking with Mercy and Esther on Thursday said he would deal with anyone who tried to come close or have a relationship with Mercy if he’s evicted on Sunday.

“If I get evicted and any guy comes close to Mercy, I will run the guy down outside the house.

“There are no rules outside the house, if you do anything, when you come out, I’ll face you,” Ike said.

Ike alongside Tacha, Cindy and six other big Brother Naija, BBNaija housemates have been selected for possible eviction this week.

Facebook Comments
Continue Reading

Entertainment

Adeniyi Johnson reacts as Ex-wife, Toyin Abraham welcomes baby

Published

on

Toyin Abraham’s ex-husband, Adeniyi Johnson on Thursday congratulated her on the arrival of her baby boy.

DAILY POST had reported that the actress welcomed a baby boy on Wednesday.

The development followed pictures of her wedding to a colleague, Kolawole Ajeyemi, which surfaced some weeks ago.

The 34-year-star was previously married to Nigerian actor, Adeniyi Johnson, from 2013 to 2015.

Friends and colleagues have congratulated her on the birth of her son by posting photos from her baby shower.

Reacting, Adeniyi on Instagram wrote, ”Congrats on the arrival of your baby. Mr &Mrs Ajeyemi . He shall be a source of joy to you. God bless the baby, the mother and the dad.

Facebook Comments
Continue Reading

Entertainment

Fans Want DJ Arafat’s Funeral Held Inside Stadium

Published

onThousands of heartbroken fans of late Ivory Coast musician, DJ Arafat, have signed an online petition asking the country’s Ministry of Culture to use their biggest stadium to hold his funeral service.

The 33-year-old artistes died on Monday morning after a motorbike accident in Abidjan, the country’s capital.

Originally known as Ange Didier Huon, DJ Arafat was famous for his energetic dance steps and scintillating brand of coupé-décalé sound that left fans begging for more.

Over 65,000 people have signed the petition on change.org asking for the Félix Houphouet Boigny Stadium to be used for the funeral, according to a BBC report on Wednesday.

Facebook Comments
Continue Reading
Advertisement
Advertisement

Trending

%d bloggers like this: