Amnesty: ‘Jami’an tsaro sun ci zarafin ‘yan Shi’a’

Jami'an tsaron Najeriya

Ba wannan ne artabun jami’an tsaro da mabiya darikar Shi’a a Abuja ba, wadanda ke kiran a saki jagoransu Ibrahim El-Zakzaky da ake tsare da shi tun shekarar 2015

Kungiyar kare hakkin dan adam ta Amnesty International ta ce bincikenta da ta gudanar ya nuna cewa amfani da karfin da ya wuce kima da sojoji da ‘yan sandan Najeriya suka yi ne ya kai har aka kashe akalla mabiya kungiyar ‘yan uwa musulmi ta Shi’a 45 a kwanaki biyu da suka gudanar da muzahara a birnin Abuja

Amnety ta ce jami’anta masu bincike sun ziyarci wurare guda biyar a Abuja da kuma cikin jihar Nasarawa inda mabiya Shi’a da suka ji rauni ke karbar magani, da kuma wurare biyu da aka ajiye gawawwakin wadanda suka mutu.

Kungiyar ta ce jami’anta sun tattauna da wadanda rikicin ya rutsa da su, da jami’an lafiya tare da yin nazari ga hotuna da bidiyo na wadanda suka ji rauni da wadanda aka kashe a lokacin zangar-zagar a ranar asabar da kuma litinin.

Babban daraktan kungiyar a Najeriya Osai Ojigho ya ce hotunun sun nuna yadda jami’an tsaro suka tarwatsa gangamin ‘yan Shi’a ta hanyar bude wuta ba tare da wani gargadi ba wanda ya ce ya sabawa dokar Najeriya da ta duniya.

Amnesty ta ce akalla masu zanga-zanga 122 suka ji rauni ta hanyar harbin bindiga yayin da kuma 39 suka mutu a artabun da aka yi tsakanin ‘yan kungiyar ‘yan uwa musulumi da ke zanga-zanga da jami’an tsaro a ranar litinin.

Amnesty ta kara da cewa ta na da shaidun da suka nuna ‘yan sanda sun yi harbin kan mai tsautsayi, alhalin masu zanga-zangar ba sa dauke da makamai.

Amma a bangaren gwamnati Ministan tsaron Najeriya, Birgediya Janar Mansur Dan Ali mai ritaya, ya ce sojoji ba su yi amfani da karfin da ya wuce kima ba wajen tunkarar daruruwan ‘yan shia’ar, inda ya zargi ‘yan kungiyar da daukar doka a hannunsu.

To sai dai Amnety ta yi kira ga hukumomin Najeriya su gudanar da bincike kan hakan, tare da hukunta jami’an tsaro da suka bude wa ‘yan Shi’ar wuta da kuma kwamandan da da ya basu umarni.

More News

Majalisar dokokin jihar Kaduna ta nemi ma’aikatar kudin jihar ta miÆ™ata bayanan bashin da El-Rufai ya ciwo

Majalisar dokokin jihar Kaduna ta nemi ma'aikatar kudi ta jihar da ta miƙa mata cikakken bayani kan basukan  da gwamnatin tsohon gwamnan jihar, Nasiru...

An dakatar da ayyukan kamfanin jiragen sama na Dana Air

Festus Keyamo, ministan harkokin sufurin jiragen sama ya umarci hukumar FAAN dake lura da sufurin jiragen sama a Najeriya ta dakatar da ayyukan kamfanin...

Yahaya Bello Ya Bayyana Dalilan Da Ya Hana Shi Bayyana A Gaban Kotu

Tsohon gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello ya ce tsoron kamun  hukumar EFCC dake yaÆ™i da yiwa tattalin arzikin Æ™asa ne ya hana shi bayyana...

Ƴan sanda sun kama mutane biyu dake samarwa ƴan fashin daji makamai a jihar Kaduna

Rundunar Æ´an sandan jihar Kaduna ta ce tana tsare da wasu mutane biyu da ake zargi da safarar bindiga a jihar. A wata sanarwa ranar...