Ambaliyar ruwa ta yi sanadin mutuwar mayaƙan Boko Haram ‘sama da 100’

Asalin hoton, Nig Army

Gwamman mayaƙa masu iƙirarin jihadi na Ƙungiyar Boko Haram sun mutu a ruwa yayin da suke guduwa daga hari ta sama da ƙasa da sojojin Najeriya ke yi musu a Jihar Borno.

Jami’an tsaron ƙasar sun ce sun kai hari ne a maɓoyar mayaƙan a can cikin dajin Sambisa.

Rahotanni sun ce baya ga farmakin sojojin, akwai ɗaruruwan mayaƙan da suka tsere tare da iyalansu sakamakon ambaliyar ruwa da ta mamaye sansanoninsu.

Mayaƙan sa kai waɗanda ke yaƙar ƴan Boko Haram din sun bayyana cewa sun zaƙulo gawarwaki sama da 100 daga cikin kogi inda suka binne su.

Karin wasu labaran da za ku so ku karanta

Rahotanni sun ce ambaliyar da Kogin Yedzaram ya yi ne ya jawo ambaliyar da ta shafi sansanonin mayaƙan da dama, lamarin da ya ja suka yi hijira.

Dubban mutane ne dai suka mutu, kuma kusan mutum miliyan biyu ne mayaƙan na Boko Haram suka raba da muhallansu.

Sai dai a ƴan kwanakin nan jami’an tsaron ƙasar sun ce ana samun sauƙi sakamakon irn farmakin da suke kai wa mayaƙan.

Haka kuma ana samun wasu daga cikin mayaƙan na Boko Haram da suke tuba suna miƙa wuta.

Kazalika wasu kuma sun bazama inda suke haɗewa da wasu ƙungiyoyi masu iƙirarin jihadin irin su ISWAP da ta fi ƙarfi a arewa maso gabas da kuma ANSARU da ke da ƙarfi a arewa maso takiya da kuma wani fanni na arewa maso yammacin Najeriya.

More News

EFCC na neman Yahaya Bello ruwa a jallo

Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arzikin Kasa Ta’annati (Economic and Financial Crimes Commission) ta bayyana tsohon gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello a matsayin...

Mutane da dama sun mutu bayan motar fasinja ta taka bam a Borno

Akalla mutane 16 ne ake fargabar sun mutu yayin da wasu 20 suka jikkata bayan wata motar fasinja da ke kan titin Baga-Kukawa a...

Sojoji Sun Ceto Lydia Simon Ɗaya Daga Cikin Ƴan Matan Chibok

Dakarun sojan Najeriya dake aiki da rundunar samar da tsaro ta Operation Desert Sanity III sun samu nasarar ceto, Lydia Simon ɗaya daga cikin...

Gwamna da ƴansanda sun daƙile yunkurin EFCC na kama Yahaya Bello

A ranar Laraba ne Gwamnan Jihar Kogi, Usman Ododo, ya dakile wani yunkurin da Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arzikin Kasa Ta’annati ta...