Ambaliyar ruwa ta tafi da wata gada a jihar Kebbi

Mamakon ruwan sama da aka fara da daren ranar Alhamis da aka cigaba da sheƙawa har tsakar  ranar Juma’a ya jawo karyewar wata gada a ƙaramar hukumar Maiyama dake jihar Kebbi.

A cewar wasu majiyoyi dake yankin da abun ya faru gadar wacce ta haɗa ƙauyukan Sambawa, Gumbin-Kure, Uguwar Shuaibu, da kuma Gandiji ta karye a ranar Juma’a sakamakon ruwan da ake yi.

Wani mazaunin yankin ya ce gadar wacce babban hanyar sufuri ce da al’ummomin ke amfani da ita kuma karyewarta ya jawo tsaiko  kan sha’anin tattalin, al’amuran yau da kullum  ayyuka masu muhimmanci kamar zuwa asibiti ga al’ummar yankin dama waɗanda ke kewaye da su.

Wani jami’in ƙaramar hukuma ya faɗawa wakilin gidan jaridar Daily Trust cewa hukumomi sun fara aiwatar da aikin ceton gaggawa.

Inda ya ce tuni aka kwashe wasu mutanen da lamarin ya rutsa da su kuma ana cigaba da auna yawan ɓarnar da aka samu sanadiyyar karyewar gadar.

More from this stream

Recomended