Alamomi 4 na kansar bakin mahaifa

Kansar bakin mahaifa

Asalin hoton, Getty Images

Cutar daji kan kama bakin mahaifar mace, wato hanyar da É—a ke fitowa daga mahaifarta.

Majalisar Ɗinkin Duniya ta ware ranar 17 ga Nuwamba domin yaƙi da cutar kansar bakin mahaifa ta duniya kuma domin tunawa da ranar farko da aka fara fafutikar kawo karshen cutar a duniya.

A wannan rana dai ana kokarin wayar da kan mata domin sanin yadda za su kare kai daga kamuwa da cutar, da muhimmancin yin gwaji da zarar sun fara fuskantar wasu sauye-sauye a jikinsu musamman zubar jini.

Majalisar Dinkin Duniya ta yi kiyasin cewa a shekarar da ta gabata akalla akwai mata dubu 604,237 da aka tabbatar sun kamu da cutar Kansar bakin mahaifa a duniya.

Hukumar Lafiya ta Duniya WHO, ta ce kashi 99 cikin É—ari na matan da ke kamuwa da kansar bakin mahaifa na da Æ™wayar cutar ‘human papillomavirus ko HPV, wadda Æ™wayar cuta ce da ake saurin É—auka ta hanyar saduwa.

Duk da cewa sau da yawa ƙwayar cutar kan mutu da kanta kuma ba lallai ta jawo wasu alamomi ba a jiki, idan ta daɗe a jikin mace ta kan haifar da kansar bakin mahaifa.

Kansar bakin mahaifa ita ce cutar daji ta huÉ—u mafi shahara da ke kama mata. Shi ya sa ma aka ware watan Janairu don wayar da kan al’umma kan wannan cuta.

WHO ta ce a shekarar 2018, an yi ƙiyasin mata 570,000 ne aka gano suna ɗauke da kansar bakin mahaifa a faɗin duniya kuma mata 311,000 ne cutar ta kashe.

Dokta Zainab Shinkafi-Bagudu, shugabar ƙungiyar Medicaid mai bincike da tattara alƙaluma kan cutar daji a Najeriya ta ce ya fi dacewa mata su riƙa zuwa ana tantance su ba sai sun ga alamomin cutar ba.

“Da zarar mace ta fara saduwa da namiji ya kamata ta riÆ™a zuwa asibiti ana mata gwaji a kai a kai. Ta hanyar gwajin nan ne za a gani idan da cutar a jikinta.

“Kuma kansar bakin mahaifa na da saurin warkewa idan har an gano ta wuri, wato idan ba a bari ta yi yawa ba. Shi ya sa muke cewa a riÆ™a tantancewa,” a cewar likitar.

WaÉ—anne ne manyan alamomin kansar bakin mahaifa?

Ganin jini a lokacin da ba na al’ada ba

Wannan na É—aya daga cikin alamomin farko-farko da mace za ta gani.

Ta kan ga jini kafin ko bayan al’ada a matan da ke shekaru haihuwa, wato dai a lokacin da ba su saba ganin jininsu na al’ada ba. Wannan jinin na iya zama da yawa ko kaÉ—an.

Wani lokaci, jinin kan fara zuba ne da zarar an gama saduwa.

A matan da suka kai shekarun É—aukewar al’ada ma, zubar jinin ne alama ta farko.

Likitoci sun ce idan mace ta kai shekarun É—aukewar al’ada, ko yaya ta ga jini daga al’aurarta ta gaggauta zuwa asibiti saboda alama ce da ke nuna cewa akwai wata matsala.

Sai dai ba ko yaushe ne wannan alama ke zama ta kansar bakin mahaifa ba.

Akwai cutukan da kan zo da irin waÉ—annan alamomin.

Wata alama da dajin bakin mahaifa kan zo da shi iat ce ruwan da ke zuba daga al’aurar mace kan Æ™ara yawa fiye da yadda ta saba gani. Kuma wani lokaci ya kan zo da wari.

Ciwon baya da ƙafa da mara

Idan kansar bakin mahaifa ta fara yaɗuwa sosai, mace kan ji ciwon ƙafa da ciwon baya da ciwon mara sosai.

Wani lokaci ma ƙafa ɗaya ko duka ƙafafuwan biyu kan kumbura baya ga yawan ciwo da zugi.

Wannan na faruwa ne idan cutar dajin ta danno wata jijiya da ke haɗe da ƙafa da mara da baya.

Haka kuma, a kan ji zugi ko nauyi a mara daga ƙasan cibiya.

Mata da yawa masu wannan cuta na bayyana yadda suke ji a mararsu kamar ana tsira masu wani abu mai tsini, sannan zugin kan daÉ—e wani lokaci kuma ya kan É—auke sannan ya dawo.

Asalin hoton, Getty Images

Matsalar fitsari da bayan gida

Wannan na iya zama jin zafi a lokacin yin fitsari ko bayan gida. Wani lokaci kuma, fitsari ko bayan gida kan fita daga jikin mace ba tare da saninta ba.

Wato zai zamo ba ta iya riƙe fitsari da bayan gida.

Wannan na faruwa ne idan dajin ya yi girman da har ya shafi ƙoda da mafitsara da hanji.

Duk da dai ba a fiye gani ba, kansar bakin mahaifa kan danne hanyoyin fitsari da bayan gida har mace ta kasa yin ko wanne daga cikinsu.

Jin zafi a lokacin saduwa

Kansar bakin mahaifa kan sa mace jin zafi ko raÉ—aÉ—i a lokacin saduwa.

Wannan raÉ—adi na iya kasancewa a al’aura ko a mara.

Likitoci sun ce da zarar mace ta ji haka, ta je asibiti ta bayyana wa likita.

Da yawa daga cikin waÉ—annan alamomi na bayyana ne idan cutar ta yi nisa.

Amma Dokta Zainab Bagudu ta ce tun kafin a ji alamomi ya kamata a je asibiti.

“Yanzu akwai riga-kafi da aka samu na wannan cuta. Da zarar yarinya ta kai shekara 9, kafin ta fara saduwa da namiji ake yi mata.

“Wannan zai rage yaÉ—uwar wannan cuta sosai, saboda riga-kafin na matuÆ™ara taÆ™aita illar da cutar ke yi a jiki,” a cewarta.

“Asali ma, idan aka dage da karabar allurar za mu iya kawo Æ™arshen cutar kansar bakin mahaifa gaba É—aya a duniya,” in ji Dokta Zainab.

Amma ga matan da suka riga suka fara saduwa, likitar ta ce abin da ya fi shi ne yawan tantancewa da ake yi a asibiti.

Da an ga alamomin cutar a bakin mahaifarta, akwai taimako da ake bayarwa wanda zai hana ta yaÉ—uwa ta zama daji.

More News

MTN yana ƙoƙarin ƙara kuɗin kati da data a Najeriya

Katafaren kamfanin sadarwa na MTN na kokarin kara kudin katin waya da na data a Najeriya. Kamfanin sadarwa mafi girma a nahiyar Afirka ya ba...

Gwamnatin Kano Ta Rage ₦500,000 A Kuɗin Aikin Hajjin Bana

Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf ya sanar da yiwa maniyatan Aikin Hajji da suka fito daga jihar kyautar ₦500,000 domin su cika kuɗin...

Ƴan bindiga sun sace wani limami a jihar Kogi

Ƴan bindiga sun yi garkuwa da Quasim Musa babban limamin garin Iyara dake ƙaramar hukumar Ijumu ta jihar Kogi. Lamarin ya faru ne a ranar...

Delta: An dawo da gawarwakin sojojin da aka kashe Abuja don yi musu jana’iza

Gawarwakin sojojin da aka kashe a jihar Delta kwanan nan sun isa maƙabartar sojoji ta kasa da ke Abuja. Gawarwakin sun iso ne da misalin...