‘Akwai yiwuwar Najeriya ta ci gaba da ciyo bashi don biyan tallafin mai’

Akwai yiwuwar Najeriya ta ci gaba da ciyo bashi domin ci gaba da biyan tallafin man fetur, a cewar fadar shugaban ƙasa.

Mai magana da yawun Shugaba Buhari, Femi Adesina, shi ne ya bayyana hakan yayin da yake magana ta cikin shirin Sunrise Daily na gidan talabijin na Channels TV da safiyar Laraba.

A cewrsa: “Ko ma dai yaya ne dole ne Najeriya ta ji a jikinta. Ko dai mu ɗanɗana kuɗarmu a matsayinmu na ‘yan ƙasa…ko kuma gwamnati ta ci gaba da ciyo bashi, wanda ba zai yi wa gwamnatin tarayya da jihohi kyau ba a tattalin arziki.

“Kun san irin yawan kuɗin da za a adana idan aka soke tallafin sannan kuma a saka su cikin wani fannin na ƙasa. Idan ba a yi hakan ba a yanzu – na yarda ba abu ne mai sauƙi ba a yanzu – to fa dole ne mu ɗanɗana kuɗarmu.”

A shekarar da ta gabata Majalisar Dattawa ta amince wa gwamnatin Buhari ta ciyo bashi iri-iri, ciki har da na dala biliyan 6.1, sai kuma na dala biliyan 16 da wani na yuro biliyan ɗaya a watannin Yuli da Nuwamba kowannensu.

Akwai yiwuwar gwamnati ta kashe naira tiriliyan biyu da rabi cikin shekara ɗaya da rabi da gwamnatin ta ce za ta ci gaba da biyan tallafin.

More from this stream

Recomended