Akwai jan-aiki a gabanmu a La Ligar bana – Suarez | BBC Hausa

'Yan wasan tawagar Barcelona

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Har yanzu Barca ba ta ci wasan waje ba a La Liga

Dan wasan gaban Barcelona Luis Suarez ya ce “akwai jan-aiki” a gaban kungiyarsu a La Liga ta bana biyo bayan rawar da suka fara takawa mafi muni cikin shekara 25.

Tawagar Ernesto Valverde, wadda ita ce zakarar La Liga sau hudu cikin biyar na baya bayan nan, ta sha kashi a karo na biyu a bana a hannun Granada ranar Asabar kuma ta koma mataki na bakwai.

Maki bakwai da Barca ta samu a wasa biyar na bana shi ne mafi karanci da ta samu a farkon gasar La Liga tun a shekarar 1994/1995 a karkashin mai horarwa Johan Cruyff.

“Rashin nasarar abin damuwa ne kwarai, babu dadi,” Suarez ya shaida wa AS.

“Ya kamata mu kalli abin da niyyar gyara abubwa da dama. Akwai jan-aiki a gabanmu amma irin wadannan wasannin su ne za su ba ka nasara a lig.

“Lallai sai mun kara azama idan muna son mu ci lig.”

Barcelona tana fama a wasannin waje bayan shafe wata biyar ba tare da cin wasa ba, sannan kuma ba ta ci kwallo ko daya ba a wasa shida na baya-bayan nan a La Liga.

More News

Majalisar dokokin jihar Kaduna ta nemi ma’aikatar kudin jihar ta miƙata bayanan bashin da El-Rufai ya ciwo

Majalisar dokokin jihar Kaduna ta nemi ma'aikatar kudi ta jihar da ta miƙa mata cikakken bayani kan basukan  da gwamnatin tsohon gwamnan jihar, Nasiru...

An dakatar da ayyukan kamfanin jiragen sama na Dana Air

Festus Keyamo, ministan harkokin sufurin jiragen sama ya umarci hukumar FAAN dake lura da sufurin jiragen sama a Najeriya ta dakatar da ayyukan kamfanin...

Yahaya Bello Ya Bayyana Dalilan Da Ya Hana Shi Bayyana A Gaban Kotu

Tsohon gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello ya ce tsoron kamun  hukumar EFCC dake yaƙi da yiwa tattalin arzikin ƙasa ne ya hana shi bayyana...

Ƴan sanda sun kama mutane biyu dake samarwa ƴan fashin daji makamai a jihar Kaduna

Rundunar ƴan sandan jihar Kaduna ta ce tana tsare da wasu mutane biyu da ake zargi da safarar bindiga a jihar. A wata sanarwa ranar...